Dollar
35,1560
-0.21 %Euro
36,6435
-0.23 %Gram Gold
2.960,9600
-0.08 %Quarter Gold
4.908,6300
0.00 %Silver
33,5600
-0.03 %"Bayanan da aka tattaro sun nuna cewa cikin sa’o’i 24 da suka wuce, na samu tashe-tashen hankula 236 a faɗin ƙasar Mozambique inda mutum 21 suka rasu," in ji Ministan Cikin Gida Pascoal Ronda.
Rikicin da ya mamaye Mozambique bayan Ƙotun Ƙolin ƙasar ta tattabar da ɗan takarar jam’iyya mai mulki Daniel Chapo a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 9 ga watan Oktoba ya kashe aƙalla mutum 21 ciki har da ‘yan sanda biyu, in ji hukumomi.
Ministan harkokin cikin gidan Mozambique Pascoal Ronda ya shaida wa manema labarai a Maputo da yammaci ranar Talata cewa sanarwar kotun ce ta yi silar a tashe-tashen hankula.
Ya ce galibin tashe-tashen hankulan sun samu jagorancin matasan da ke goyon bayan ɗan takarar da ya sha kaye Venancio Mondlane ne, wanda ya samu kashi 24 cikin 100 na ƙuri’u, bayan Chapo, wanda ya samu ƙuri’u kashi 65 cikin 100.
"Daga ra’ayin jama’a da aka fara tattarawa dai cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an gano cewa an samu tashe-tashen hankula 236 a faɗin ƙasar, lamarin da ya janyo mutuwar mutum 21, inda biyu daga cikinsu suka kasance ‘yan sandan Mozambique," in ji Ronda.
Ya ce farar-hula 13 da ‘yan sanda 12 ne suka jikkata sakamakon rikicin.
Ronda ya ce an ƙona motoci 25 ciki har da motocin ‘yan sanda biyu.
Ya ƙara da cewa an far wa ofisoshin ‘yan sanda da kuma gidajen gyaran hali 11 inda aka kwashe kayayyaki tare da kuɓutar da fursunoni.
Tashin hankali
Hankulan mutane sun tashi a ƙasar gabanin hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar ranar Litinin, kuma an fara samun zanga-zanga bayan an sanar da hukuncin.
Bidiyoyin da suke karaɗe shafukan sada zumunta sun nuna masu zanga-zanga suna ƙona tare da kwashe kayayyaki daga shaguna a babban birnin ƙasar Maputo, da kuma birnin Beira, inda rahotanni suka ce wasu jami’an birnin sun tsere.
Mondlane ya yi kira da “rufe ko ina” daga ranar Juma’a, amma rikicin da ya ɓarke a ƙasar ya riga ya ta’azzara kuma ana zaman ɗarɗar a babban birnin ƙasar ranar Talata da daddare bayan an wuni ana rikici.
‘Yan adawa da kuma masu sa ido a zaɓe sun yi ta zargin Frelimo da tafka maguɗi a zaɓen. Amma ya musanta zargin.
Comment