Sport
Dollar
35,5594
0.16 %Euro
36,5618
-0.36 %Gram Gold
3.091,7000
-0.06 %Quarter Gold
5.064,8900
0.14 %Silver
34,6700
-1.25 %Rahotanni sun ce tankar man ta yi bindiga ne bayan wani ƙaramin hatsari da ta samu, inda jama’ar da ke kusa da wurin suka je kwalfar fetur ɗin da ke cikin tankar.
Wata tankar mai wadda ke cike da man fetur ta yi bindiga a ranar Asabar a kusa da Dikko Junction da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a wanda ke a Jihar Neja.
Rahotanni sun ce tankar man ta yi bindiga ne bayan wani ƙaramin hatsari da ta samu, inda jama’ar da ke kusa da wurin suka je kwalfar fetur ɗin da ke cikin tankar.
Aƙalla mutum 50 ne suka rasu sakamakon fashewar tankar man, kamar yadda kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta jihar Neja Kumar Tsukwam ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya
Gwamnan Jihar Neja Umaru Bago ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa a sanarwar da sakataren watsa labaran Bologi Ibrahim ya fitar.
Ana yawan samun fashewar tankar mai bayan ta yi hatsari a Nijeriya inda jama'a da dama da ke zuwa kwalfar man fetur ke mutuwa.
Ko a kwanakin baya sai da fiye da mutum 100 suka rasu a gobarar tankar mai a Jigawa.
Comments
No comments Yet
Comment