Dollar

35,4431

0.27 %

Euro

36,3540

-0.47 %

Gram Gold

3.063,1500

1.01 %

Quarter Gold

4.997,4300

-0.04 %

Silver

34,5800

1.03 %

Continents

Categories

Rahotanni daga Gaza sun ce sojojin Isra'ila sun harbe ɗan jaridar ne a daidai lokacin da yake a bakin aiki yana ƙoƙarin haɗa wani rahoto.

Isra'ila ta kashe ɗan jaridar kamfanin dillanacin labarai na Anadolu a Gaza

Isra’ila ta kashe wani ɗan jarida mai zaman kansa na kamfanin dillancin labarai na Anadolu mai suna Saed Abu Nabhan a Gaza.

A ranar Juma’a, sojojin na Isra’ila sun soma yin ƙawanya ga wani wuri a sansanin gudun hijira na Al-Jadeed, wanda ke a tsakiyar yankin Nuseirat da ke Gaza, inda wuri ne da ‘yan jarida da dama ke a wurin kafin kai hari.

Wani bidiyo da aka ɗauka ya nuna wani mutum wanda aka ji wa rauni an ɗauke shi bisa makara tare da taimakon jami’an lafiya.

Sai a cikin bidiyon aka ga Abu Nabhan wanda ɗan jarida ne mai ɗaukar hoto yana ƙoƙarin ɗaukar bidiyo da kayan aikinsa kawai sai aka ga an harbe shi da bindiga.

Sai aka ga Abu Nabhan ya faɗi ƙasa inda ya yi kwance babu motsi.

Sai mutanen da ke kusa suka yi ƙoƙarin zuwa wurin shi amma suna tsoro domin kada harsashi ya same su.

Kamfanin dillancin labarai na Wafa ya tabbatar da harin inda ya bayar da tabbacin kisan Abu Nabhan.

Wannan kisan da Isra'ila ta yi wa Abu Nabhan ya kawo adadin 'yan jaridar da ƙasar ta kashe zuwa 203 tun daga 7 ga Oktoban shekarar 2023.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet