Dollar

35,1761

-0.01 %

Euro

36,7640

0.01 %

Gram Gold

2.956,9600

-0.70 %

Quarter Gold

4.901,0500

-0.09 %

Silver

33,2100

-1.47 %

Continents

Categories

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 449 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 45,436 tare da jikkata fiye da mutum 108,038. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,048 tun da ta soma kai hare-hare a Oktoban 2023

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 11 a sabin hare-haren da ta kai a Gaza

0750 GMT — Akalla Falasdinawa 11 ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan fararen hula a arewacin Gaza, da wani gida da ke tsakiyar gabar tekun, da kuma tantunan mutane da ke Khan Younis, inda ake fargabar adadin wadanda suka mutu ya karu.

Majiyoyin lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, wani harin da Isra'ila ta kai kan wasu fararen hula a titin Sarari da ke Jabalia a arewacin Gaza, ya kashe Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu da dama.

An kashe karin Falasdinawa tara da suka hada da kananan yara a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan gidan iyalan Naami da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Maghazi da ke tsakiyar Gaza.

0721 GMT — Isra'ila ta tsare daraktan wani asibiti a Gaza

Jami'an kiwon lafiya na Gaza sun ce sojojin Isra'ila sun tsare daraktan wani asibiti a arewacin kasar, wanda hukumar lafiya ta duniya ta ce wani hari da Isra'ila ta kai ya hana shi aiki.

Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta Gaza ta fitar ta ce "Dakarun Isra’ila sun kwashe da yawa daga cikin ma'aikatan lafiya daga asibitin Kamal Adwan zuwa wurin tsare mutane domin yi musu tambayoyi, ciki har da darakta Hossam Abu Safiyeh."

Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta kuma bayar da rahoton cewa, an tsare Abu Safiyeh, inda ta kara da cewa daraktan hukumar a arewacin kasar, Ahmed Hassan al-Kahlout na cikin wadanda ake tsare da su.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet