Dollar

35,2388

0.21 %

Euro

36,7358

0.10 %

Gram Gold

2.982,7000

0.16 %

Quarter Gold

4.905,4200

0.00 %

Silver

33,8700

0.48 %

Continents

Categories

Tsohon shugaban ƙasar tsakanin 2012 zuwa 2017, Mahama, mai shekaru 65, ya samu kuri'u miliyan 6.3, wato kashi 56.5% na ƙuri'un da aka kaƙa, in ji hukumar zaɓen ƙasar.

Mahama ya lashe zaɓen Ghana da 57% na ƙuri'un da aka kaɗa: Hukumar Zaɓe

An ayyana tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da yammacin Litinin, bayan da masu kaɗa kuri'a suka nuna fushinsu kan yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arzikin ƙasar.

Tsohon shugaban ƙasar tsakanin 2012 zuwa 2017, Mahama, mai shekaru 65, ya samu kuri'u miliyan 6.3, wato kashi 56.5% na ƙuri'un da aka kaƙa, in ji hukumar zaɓen ƙasar.

Babban abokin hamayyar Mahama, Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia, ya amince da shan kaye a ranar Lahadi. Bawumia ya samu kuri'u miliyan 4.6, wato kashi 41%.

Yawan ƙuri’un da aka kaɗa a mazaɓu 267 ya kai kashi 60.9%, in ji Shugaban Hukumar Zaɓen Ƙasar Jean Mensa. Mensa ta ƙara da cewa duk da cewa ana ci gaba da ƙidayar kuri'u a mazabu tara, amma hakan ba zai sauya sakamakon ƙarshe ba.

‘Nasarar’ a bayyane

Mahama ya bayyana nasarar da ya samu a matsayin "mai matukar muhimmanci." Ya yi alkawarin "sake gina" ƙasar ta bangarori daban-daban a lokacin yakin neman zabe, wanda ya ba da fifiko ga tattalin arziki da kuma kira ga matasan Ghana da ke kallon kuri'un a matsayin hanyar fita daga matsalar tattalin arzikin kasar.

An dai gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tsadar rayuwa mafi muni a cikin tsararraki.

Ana yi wa zaben kallon tamkar wani gwaji ne na dimokuradiyya a yankin da tashe-tashen hankula da juyin mulki suka girgiza. Kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka ta ce gaba ɗaya zaben ya gudana cikin lumana, wanda ke ci gaba da gudana a Ghana.

Jam'iyyar Mahama ta lashe rinjayen 'yan majalisa

Bawumia dai ya tsaya takarar ne a tutar jam'iyyar New Patriotic Party, ko NPP mai mulki, wacce ta yi ta fama da matsalar tattalin arziki a karkashin shugaba mai barin gado Nana Akufo-Addo.

Jam'iyyar Mahama ta National Democratic Congress ita ma ta samu rinjaye a majalisar, in ji shi.

Ana kallon nasarar da Mahama ya samu a matsayin sabon salo na zabuka a duniya, wanda ke fifita jam'iyyun adawa fiye da masu mulki, daga Amurka zuwa kasashen Turai - irin su Birtaniya da Faransa - da kuma Afirka ta Kudu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet