Dollar

35,4227

0.23 %

Euro

36,4997

-0.04 %

Gram Gold

3.042,6800

0.34 %

Quarter Gold

4.999,3000

0.00 %

Silver

34,5100

0.83 %

Continents

Categories

Yawan barin Nijeriya da jami'an lafiya ke yi zuwa ƙasashen da suke zabarinsu da albashi mai tsoka da kyakkyawan tsarin aiki, yana janyo rashin wadatar ma'aikata a asibitocin da ke fama da yawaitar marasa lafiya.

Matsalar ƙaurar ma'aikatan lafiya na ci wa Nijeriya tuwo a ƙwarya

Daga Mazhun Idris

Matsalar ƙaurar ma'aikatan lafiya ta fara ne kusan shekaru arba'in da suka gabata, inda tsirarun ƙwararrun jami'an lafiya suka fara tafiya ƙasashen waje don neman kyawawan damarmaki. A yanzu batun na ƙara yin ƙamari.

Likitoci da ma'aikatan asibiti suna tururuwar barin ƙasar saboka kwaɗayin albashi mai tsoka, da kyakkyawan tsarin aiki, da kayan aiki, da ingantacciyar rayuwar ƙasar waje. Sai dai sashen kiwon lafiyar ƙasarsu yana karaya saboda ƙarancin ƙwararru.

Nijeriya ce ƙasar Afirka mafi yawan jama'a, da al'umma miliyan 230, kuma tana fama da tarin ƙalubalen rayuwa.

Sashen kiwon lafiya ba shi da isassun jami'ai saboda yawan marasa lafiya da asibitoci ke samu.

Ministan lafiya da walwalar jama'a na Nijeriya, Dr Muhammad Ali Pate yana yawan yin kalamai kan matsalar ƙaurar ma'aikata da ke cutar da muradun kiwon lafiya na ƙasar.

Ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Ana zabarin likitoci da ma'aikatan jinya na Nijeriya zuwa wasu ƙasashe, ta hanyoyin ɗaukar aiki da ba su dace ba", sannan ya ja hankalin jami'an lafiyar da suka zaɓi barin ƙasar bayan samun horo a gida.

A yanzu, ta yaya gwamnati za ta rage tasirin yawaitar ƙaurar ma'aikata, idan ba za ta iya hana hakan bakiɗaya ba?

Dr Pate ya ba da misalan "shirye-shiryen gyara" da ma'aikatarsa ke aiwatarwa don kawo ƙarshen matsalar.

Asibitocin gwamnati da dama a faɗin ƙasar suna fama da ƙarancin ƙwararrun ma'aikata, wadda ke shafar ɓangaren kiwon lafiya, kuma yake haifar da dogayen layuka na marasa lafiya masu jiran ganin likita.

Ƙalubalen tattalin arziƙi da matsalar ke haifarwa tana bayyana a wurare da dama.

Sannan ga ƙarancin ma'aikata da ke haifar da tsanantar cututtuka da asibitoci ba sa iya kulawa saboda ƙarancin jami'an kiwon lafiya.

Masana sun ce wani ma'aunin walwalar al'umma a cikin ƙasa shi ne kyawun harkar lafiya, wadda kuma yake shafar yawan mace-mace na al'ummarta.

Matsalar ƙaura

Wannan batu yana shafar yawancin jami'an kiwon lafiya a Nijeriya waɗanda suka yi ƙaura zuwa ƙasashen waje don yin aiki a fannonin kiwon lafiya na can.

Duk da matakin barin gida abu ne mai rikici, sukan zaɓi barin wajen aiki mai tsauri da ƙarancin kayan aiki a ƙasarsu, don karɓar ayyuka masu gwaɓi da ke zuwa da fatan samun ingantacciyar rayuwa da damarmakin haɓaka aikinsu a ƙasashen da suke tafiya.

Dr Aisha Kurfi, wata ƙwararriyar ma'aikaciyar gashin ƙashi ce da ke aiki a Burtaniya, wadda kuma ta bar Nijeriya a 2023.

Ta amsa cewa cigaba da ƙauracewa ƙasar da ƙwararru kan yi yana barazana ga sashen kiwon lafiya na Nijeriya.

Ta faɗa wa TRT Afrika cewa, "Yawaitar masu ƙaura abin tsoro ne, kuma babban abin da ke haddasa shi, shi ne albashi mai tsoka da asibitocin ƙasashen waje ke bayarwa."

Ƙasashen Amurka da Turai, inda ake saka likitocin Nijeriya cikin jerin manyan ƙwararrun ma'aikata a fannin lafiya, su suka fi morar wannan batu na ƙaurar ƙwararru daga Nijeriya.

Hukumomin Nijeriya sun ce suna inganta kayayyakin aikin lafiya don haɓaka samar da lafiya. / Hoto: Reuters

Yayin da jam'ian lafiya 'yan Nijeriya ke tallafawa fannin lafiya a waje saboda ƙwarewarsu, ayyukan asibitocin cikin gida yana taɓarɓarewa saboda ƙarancin ma'aikata, da kayan aiki da ƙaruwar buƙatar kiwon lafiya.

Babban ƙoƙarin da ma'aikatar lafiya a Nijeriya ke yi shi ne na daƙile ƙaurar ma'aikata ta hanyar inganta yanayin aikin ƙwararrun da ake raino cikin ƙasar, da kuma gina cibiyoyin lafiya.

Kaucewa rikici

Da take nuni kan muhimmancin magance matsalar kayan aiki a asibitocin gwamnati, Dr Kurfi ta ayyana batun ƙarancin kayan aiki na zamani da magunguna a asibitocin gwamnati a matsayin babban ƙalubale.

Ta faɗa wa TRT Afrika cewa, "Jami'an lafiya suna yawan ƙorafi kan wahalar aiki da rashin kyawawan damarmaki, da kuma yawaitar marasa lafiya saboda ƙarancin ma'aikata a asibitocin gwamnati".

Ministan lafiyar, Dr Pate, ya zayyana tanadin tagomashin da gwamnatin Nijeriya ke ƙaddamarwa don riƙe ma'aikatan da ke sashenta na kiwon lafiya, musamman jami'an da ke aiki a yankunan karkara.

Ya yi amanna cewa ma'aikatan da suka ƙi yin ƙaura suke aiki cikin ƙasar suna samun ƙarin karsashin yin aiki saboda cigaban da ake samarwa a yanayin aikinsu, wanda babban ƙaimi ne wajen riƙe su.

Ministan ya koka kan cewa ƙasarsa ba ta samar da wadatattun jami'ai daga makarantu lafiya da take da su, don cike guraben da ake da ƙarancin ma'aikatan lafiya. Ya ce kuma babu cibiyoin ƙara ilimi wadatattu.

Ya ce, “Muna kyautata gine-gine, kayan aiki, da gidajen ma'aikatan da ke cibiyoyin lafiya matakin farko.

"Nijeriya na cikin wani mataki na cigaba, kuma muna ƙoƙarin sake gina fannin lafiya wanda tsawon shekaru bai samu kulawa ba".

Ƙarin kasafi kuɗi

Yayin da harkar kiwon lafiya ke ci gaba da haɓaka, gwamnatin Nijeriya na neman masu zuba jari daga ƙasashen waje su shiga harkar kiwon lafiya da samar da ayyuka bisa tsarin zamani.

Sannan gwamnatin na ci gaba da ƙara jari wajen faɗaɗa shirin ba da horo ga ma'aikatan lafiya na ƙasar, da makarantun koyar da ayyukan jinya da haɗa magunguna.

Da yake kira don kawo gyara, Dr Pate ya yi fatan samun waraka mai ɗorewa kan matsalar ƙaurar ƙwararru ta hanyar inganta matakan samar da lafiya, da ɗaga darajar kayayyakin aiki, da sauya tsarin gudanarwa.

Babban jigon shirin shi ne maido da kimar aikin a idon haziƙan ma'aikatan lafiya da ke aiki cikin gida, don kawar da yiwuwar ficewar su daga ƙasar.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet