Dollar
35,2189
-0.02 %Euro
36,7902
0.00 %Gram Gold
2.966,6800
-0.06 %Quarter Gold
4.938,1500
0.00 %Silver
33,4200
-0.06 %Ganawar da suka yi a ranar Lahadi a Damascus babban birnin kasar Syria, na zuwa ne makonni biyu bayan hamɓarar da gwamnatin Bashar al Assad, shugaban Syria na kusan shekaru 25, a wani farmaki da dakarun 'yan adawa suka yi.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gana da shugaban sabuwar gwamnatin Syria Ahmad al Sharaa.
Ganawar da suka yi a ranar Lahadi a Damascus babban birnin kasar Syria, na zuwa ne makonni biyu bayan hamɓarar da gwamnatin Bashar al Assad, shugaban Syria na kusan shekaru 25, a wani farmaki da dakarun 'yan adawa suka yi.
A cewar majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Nuh Yilmaz da kuma mukaddashin mai kula da harkokin Turkiyya a ofishin jakadancin, Burhan Koroglu na cikin ganawar.
Esaad Hassan Shaibani, wanda aka nada a matsayin ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya na Syria, ya kuma gana da tawagar Turkiyya.
Wani babban jami'in diflomasiyyar Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya shi ma ya je Damascus a ranar Juma'a, a cewar ma'aikatar harkokin wajen Amurka.
Ya gana da jami'ai daga Hayat Tahrir al Sham (HTS) don tattaunawa game da buƙatar tsarin “haɗa kai” a siyasance Ganawar dai ita ce ta farko tsakanin jami'an Amurka da HTS kwanaki bayan Assad ya tsere zuwa kasar Rasha bayan da kungiyoyin da ke adawa da gwamnatin kasar suka karbe ikon Damascus a ranar 8 ga watan Disamba, wanda ya kawo karshen mulkin Jam’iyyar Baath da ke mulki tun shekara ta 1963.
Comment