Dollar
35,1761
-0.01 %Euro
36,7640
0.01 %Gram Gold
2.956,9600
-0.70 %Quarter Gold
4.901,0500
-0.09 %Silver
33,2100
-1.47 %Jam’iyyar The Front for the Liberation of Mozambique (Fremlico) ita ce ta jagoranci gwagwarmayar neman 'yancin kai daga Portugal a shekara ta 1975.
Mummunar zanga-zanga ta ɓarke a ƙasar Mozambique a ranar Litinin bayan wani hukuncin da kotu ta yanke mai cike da ce-ce-ku-ce na tabbatar da nasarar Daniel Chapo, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyya mai mulki ta Frelimco da take mulkar ƙasar tun bayan samun ‘yancin kanta.
Mintuna kaɗan bayan sanarwar, sai zanga-zanga ta ɓarke a faɗin ƙasar. An yi ta fasa bankuna da cinna wuta da yin sace-sace a ofisoshin jam’iyyar Frelimo da ofisoshin ‘yan sanda da masana’antu a faɗin ƙasar a kwanakin da suka gabata.
Fursunoni fiye da 1,500 ne suka tsere daga gidan yari mai cike da tsaro bayan da suka rusa katangarta a lokacin tashin hankalin da aka yi a ƙasar bayan sanar da sakamakon zaɓen a watan Oktoba.
Rikicin da aka yi a lokacin fasa gidan yarin ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 30 tare da jikkata mutum 15.
Amma daga baya an yi nasarar kamo fursuoni kusan 150 daga cikin wadanda suka tsere.
"Tun bayan samun ‘yancin kai wannan jam'iyyar ta (Fremlico) take mulki a Mozambique amma ta kasa miƙa wa wata jam’iyyar mulki don inganta dimokuradiyya," in ji Rufino Sitoe, wani manazarcin siyasar Mozambique, a hirarsa da TRT World.
Jam’iyyar The Front for the Liberation of Mozambique (Fremlico) ita ce ta jagoranci gwagwarmayar neman 'yancin kai daga Portugal a shekara ta 1975.
Daniel Chapo, mai shekaru 47, na Frelimo, na shirin zama shugaban kasar Mozambique na biyar.
Chapo ya samu sama da kashi 70 na kuri'un da aka kada, a cewar hukumar zaben ƙasar, yayin da Venancio Mondlane na jam'iyyar Podemos ya samu kashi 20 cikin 100. Babbar jam'iyyar adawa ta Renamo ta koma matsayi na uku.
Shugabannin jam’iyyun adawar sun yi zargin cewa an tafka magudi a zaben, kuma sun yi tir da zaben da cewa ba sahihi ba ne. Sitoe ya lura da raguwar fitowar masu jefa ƙuri'a - zuwa kashi 40 kacal a zaɓen da aka yi kwanan nan - wanda ke nuna ɓacin ran jama'a.
"Mutane suna jin cewa an yi watsi da korafe-korafensu, kuma wannan yana haifar da takaici," in ji shi.
Babban mai kalubalantar Chapo kuma madugun 'yan adawa, Mondlane, wanda a yanzu yake gudun hijira, ya bukaci magoya bayansa da su yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da zaben da ya ce an tafka magudi, yana mai gargadin "sabon boren jama'a" idan sakamakon bai canza ba.
A jawabin da ya gabatar a shafin Facebook kai-tsaye, Mondlane ya sha alwashin kafa wata gwamnatin a ranar 15 ga Janairu, ranar da Chapo zai fara aiki.
Rikicin wanda ya dauki tsawon watanni uku ya yi sanadiyar mutuwar mutum kusan 150. Yayin da kasar Mozambique ta fada cikin rudanin siyasa tun bayan zaben, zanga-zangar da aka yi a baya bayan nan da kuma fasa gidan yari da aka yi ta ce-ce-ku-ce da su sun faru ne bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da nasarar da Frelimo ta samu.
"Ina tsammanin da za a iya kauce wa hakan idan jama'a sun yi imani cewa sakamakon zaben ya kasance ingantacce ko kuma idan gwamnati ta sami hanyar sasantawa da babban dan takarar adawa don warware wannan rikicin," in ji Emilia Columbo ta Cibiyar Dabaru da Nazarin Ƙasashen Duniya da ke Washington.
“A halin yanzu, dan takarar jam’iyya mai mulki, Daniel Chapo, zai hau karagar mulki a wata mai zuwa amma zai fuskanci kalubale mai matukar wahala wajen tafiyar da kasar da ba ta amince da nasarar da ya samu ba da kuma jam’iyyar da ita ma ta samu rabuwar kawuna a cikinta kan mara masa baya a matsayin dan takara,” kamar yadda ta shaida wa TRT World.
Shanye takaici
Ana ci gaba da bayyana rashin jituwa kan nasarar jam’iyyar Frelimco wadda ta jawo fushi kan shekarun da aka shafe ana fama da cin hanci da matsin tattalin arziki da kuma kaka-gida a dimokuraɗiyya.
Karuwar samun ‘yan adawa na siyasa duk kuwa da daƙile hakan da ake yi alama ce ta irin kai mutane bango da aka yi, a cewar masana.
“Mondlane ya yi nasarar fito da fushin kowa a lokaci ɗaya,” a cewar Sitoe, mai sharhi kan al’amuran siyasa na Mozambique, yana mai nuni da karɓuwar da Mondlane ya samu duk kuwa da irin ɗumbin ƙalubalen.
“Sun ƙirƙirar masa matsaloli da yawa a takarar tasa ta shugaban ƙasa amma duk da haka sai da ya samu karɓuwa.”
Fushin da mutane suka yi ya taimaka wa Mondlane, inda ake ganinsa a matsayin babban ɗan takara mai adawa da mamayar Frelimo.
“Al’ummar ƙasar da suka bazama tituna suna tare da ra’ayinsa. Shi ya sa ake ganin wannan gagarumar zanga-zangar a Mozambique.
Kuma a yayin da ake ci gaba da wannan bore, ita ma gwamnati ba ta shirya sasanta lamarin ba,” ya bayyana, yana mai cewa gwamnati za ta yi biris da zanga-zangar ne maimakon neman mafita.
Sitoe ya ce an shafe shekaru ana fama da matsalar cin hanci, inda ‘yan ƙasar ke ganin shugabannin jam’iyyar Fremlico suna mulkin ne kawai don su azurta kawunansu.
Ta’azzarar rikici Rashin yin wani kataɓus daga bangaren gwamnatin da kuma ƙin tattaunawa da ɓangaren adawa na ƙara rura wutar rikicin.
“Hanyar da gwamnati ke bi wajen biyar da wannan lamari ba mai daɗi ba ne,” Sitoe ya koka. “Ba su nuna damuwa ba sam a kan fafutukar al’ummar Mozambique.”
Ya yi nuni da cewa magance talauci da rikice-rikice—kamar tsattsauran ra’ayi a arewacin Mozambique da kuma sace-sacen mutane a Maputo babban birnin kasar—yana da matukar muhimmanci wajen maido da kwanciyar hankali.
Rashin tattaunawa mai ma'ana ko gyare-gyare yana haifar da haɗari. "Ba a taba yin zanga-zangar lumana a nan ba saboda 'yan sanda suna kai hari ga masu zanga-zangar," in ji Sitoe.
Makoma marar tabbas?
Sitoe na hango lalacewar al’amura da ta’azzarar rikici.
"Bisa ga yadda gwamnati take ɗaukar lamarin, matsalar za ta karu ne kawai saboda ba a tattaunawa ta gaskiya," in ji Sitoe.
'Yan kasar Mozambique na fatan samun tabbacin cewa nan gaba za a samu sauki.
Amma duk da haka, Sitoe ya yi gargadin cewa, gazawar gwamnati na isar da fata ko magance korafe-korafe na nufin yanayin ya kasance mara kyau.
A ganin Sitoe, shugaban kasa da manufofin gwamnati su guji yin magana game da ainihin batun.
"Za su yi komai amma ba sa son yi magana a kan matsalar kuma ba za su saurari koke-koken jama'a ba ko kuma su yi wani abu don tabbatar wa mutane cewa abubuwa za su gyaru."
Sitoe ya kara da cewa abin da mutane suka fi bukata a yanzu shi ne su san cewa shekara mai zuwa da kuma na gaba za su fi wannan.
"Bisa ga rashin iya isar da wannan sako, za mu iya tunanin cewa abubuwa za su kara ta'azzara ne kawai a cikin kwanaki masu zuwa," in ji shi.
Comment