Dollar

35,1761

-0.01 %

Euro

36,7640

0.01 %

Gram Gold

2.956,9600

-0.70 %

Quarter Gold

4.901,0500

-0.09 %

Silver

33,2100

-1.47 %

Continents

Categories

Erdogan ya ce Turkiyya ta riƙe ’yan uwantaka, ta kuma taimaki mutanen da ake zalunta a Syria lokacin matsalar da aka shiga ta tsawon shekaru 13, sannan ta sake yin nasara.

Turkiyya za ta murƙushe ta’addanci gaba da iyakokinta na kudanci a 2025 — Erdogan

Turkiyya za ta tabbatar da tsaro gaba da iyakokinta na kudanci kuma za ta kawar da barazanar ta’addanci da ke tasowa daga waɗannan yankun, a cewar Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Da yake magana a taron Jam’iyyar AK mai mulki a wajen Babban Taronta Karo na Takwas a yankin Balikesir, kamar yadda Erdogan yake cewa: “Daga farkon 2025, za mu tabbatar da tsaro gaba da iyakokinmu na kudanci, musamman ma dangane da batun ta’addanci, mu kuma kawar da barazanar da ke tasowa daga waɗannan yankunan.”

Erdogan ya ce a shirye yake ya matso da Turkiyya kusa da burikan “Zamanin Turkiya,” a kowane ɓangare ciki, har da gudunmawa wajen kawo ƙarshen yaƙi ga “arewa”, da samun nasara a shirye-shiryenta na tattalin arziki, da ƙara samun nasarori a ɓangarori kamar na tsaro, da fasaha mai zurfi, da ƙirƙirarriyar fasa, da wuraren samun makamshi wanda zai kawar da dogaro kan ƙasashen waje.

Dangane da rushewar gwamnatin Assad a Syria, Erdogan ya ce Turkiyya “ta riƙe ‘yan uwantaka,” ta taimaki waɗanda aka zalunta, “sannan mun yin nasara.”

Shugaba Erdogan ya ce matsalar da jama’a suka shiga cikinta tsawon shekaru 13, da kuma “danniyar” ‘yan Baath ta tsawon shekara 61 a Syria sun zo ƙarshe, yayin da mutanen Syria suka ƙaddamar da juyin-juya hali a ‘yan makwannin nan, abin da ya ba da nasara cikin sauri.

Turkiyya ta karɓi baƙuncin ‘yan Syria miliyan 3.6 ta kuma tabbatar da tsaron wasu ƙarin mutum miliyam 4 a wasu ƙasashen yayin da aka fuskanci matsala a Syria, a cewar shugaban na Turkiyya. “Mun ciri tuta a fannin tallafa wa ɗan’adam da kyakkyawan sakamako.”

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet