Dollar

35,4431

0.27 %

Euro

36,3540

-0.47 %

Gram Gold

3.063,1500

1.01 %

Quarter Gold

4.997,4300

-0.04 %

Silver

34,5800

1.03 %

Continents

Categories

Me ya sa a labaran kafafane watsa labarai na ƙasa da ƙasa ba a ganin Sudan sosai, duk da miliyoyin mutane da aka jefa yunwa, aka raba su da matsugunansu, da wahalhalu marasa misaltuwa?

Yaƙin Sudan: Rikicin da aka yi biris da shi wanda ke halaka duniya

Daga Abdalftah Hamed Ali da Sarah Khamis

Yaƙin Sudan, wanda ya ɓarke a watan Afrilun 2023, ya jefa ƙasar cikin mummunan rikicin siyasa, da koma bayan tattalin tattalin arziki da jin kai. Duk da girman ibtila'in, ƙasar na gwagwarmayar janyo hankulan duniya da kafafan yada labarai na kasa da kasa, ba kamar sauran rikicin da ake ci gaba da yi a Gabas ta Tsakiya ba, ciki har da Gaza da Lebanon, da ma na baya-bayan nan Siriya.

Ƙarfin rikicin Sudan da halin da ake ciki da tasirin da yake da shi a yankin da ma duniya baki daya, abu ne da ya zama dole a kalle shi da idanuwan basira kuma cikin tsanaki. Tsawon lokaci, akwai babban gibi a yadda kafafen yada labarai na duniya ke dauko labarai game da Sudan. Me ya sa aka bar hakan na faruwa, kuma me za a yi don magance matsalar?

Mummunan halin jin kan bil'adama a Sudan

Sama da mutane miliyan 14 - kamar dai kashi 30 na jama'ar Sudan - sun rasa matsugunansu tun watan Agustan 2023, ciki har da mutum miliyan 11 a cikin gida da milyan 3.1 da suka gudu zuwa kasashe makota, in ji Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta MDD.

Anihini abin da ke girgiza kwakwalwa shi ne sama da rabin jama'ar Sudan (Kashi 53) na wadanda aka tsugunar yara ne kanana 'yan kasa da shekaru 18. Rikicin ya jefa 'yan kasar Sudan miliyan 130 cikin halin neman taimakon jin kai, inda yunwa ke addabar su musamman a sansanin ZamZam da ke Dafur ta Arewa, in ji hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.

Wadannan ba alkaluma ba ne kawai da za a yi watsi da su, amma gaskiyar ita ce; alkaluman na bayyana girman rikicin da ke azabtar da miliyoyin mutane, wanda gaza tsagaita wuta yake kara ta'azzarawa inda kuma hankalin kasashen duniya ke kara barin wajen.

Mayakan RSF da tun asali gwamnatin Sudan ta kafa wanda suke masu hatsari - na da hannu a ta'annati da dama da aka yi. Barnar da suka yi ta hada da kashe fararen hula, da yi musu fyade, da rikicin kabilanci da amfani da yunwa a matsayin makami da sauran keta hakkokin ɗan'adam.

An tsugunar da sama da mutane miliyan 11 a cikin Sudan, suna gwagwarmayar samun kayan more rayuwa. / Hoto: AFP.

A farkon watan Disamban 2024, aƙalla mutane 127 - mafi yawan su fararen hula - aka kashe a cikin kwanaki biyu da aka dauka ana ruwan bama-bamai, wanda hakan ya zama lamari mafi muni na kashe rayuka a 'yan watannin nan, kamar yadda masu kare hakkokin dan adam suka bayyana.

Wadannan munanan ayyuka wani bangare ne na gangamin da ake yi na yakar wasu kabilu, misali a Masalit, wanda masu sanya idanu na kasa da kasa suka yi gargadin cewa zai iya zam laifin zarafin ɗan'adam. Waɗanda suka tsira a Darfur sun bayyana mummunan halin da suka shiga bayan kona kauyukansu, aka tarwatsa danginsu tare da cin zarafin mata.

An kuma yi amfani da yunwa a matsayin makami a yakin. An zargi RSF da aikata munanan kisa tun bayan barkewar rikicin a 2023, inda aka samu rahotanni da yawa da ke bayyana yadda suka yi amfani da yunwatarwa a matsayin makamin yakar fararen hula da suka tirje da kuma samun iko a kan su.

Yadda 'yan tawayen suka hana a kai kayan abinci na agaji zuwa yankunan da yunwa ke addaba ya jefa miliyoyin mutane cikin yunwa. A sansanoni irin su Zamzam, dubunnan daruruwan fararen hula na fuskantar yunwa inda aka gaza kai musu abinci da magunguna.

UNICEF ta kiyasta cewa dubunnan daruruwan yara za su wahala sosai saboda tsananin karancin abinci a wannan shekarar, suna masu bayyana tsananin ibtila'in. Misali, a sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam, kusan kashi daya cikin hudu na yara kanana da aka tantance na dauke da cutar yunwa mai tsanani, in ji Likitocin da suke ba da agaji na kasa da kasa wato MSF.

Yara da dama na fama da matsananciyar yunwa, in ji likitocin MSF (AFP).

Duk da tsananin wannan rikici, rikicin Sudan na ta kokarin janyo hankalin kafafan watsa labarai na duniya. Wahalhalun da ake ci gaba da sha sun zama ba a ganinsu saboda wasu rikice-rikicen yankuna daban, inda aka bar miliyoyin 'yan Sudan ba tare da tallafi da taimakon kayayyakin da suke tsananin bukata ba. Ana bukatar babban yunkuri na bayar da fifiko ga halin da Sudan ke ciki tare da taimaka wa wadanda lamarin ya rutsa da su a matakin kasa da kasa.

Rashin zaman lafiya a yankin da tasirinsa ga sauran yankuna

Yakin Sudan ba wai ibtila'i ne na kasa kawai ba; wani babban rikici ne da ke addabar Yankin Kusurwar Afirka. Masu neman mafaka da ke guje wa rikicin sun cika kasashe makota, da suka hada da Chadi, Masar, da USdan ta Kudu. Tuntuni da ma Chadi na fama da nata matsalolin na siyasa, a yanzu kuma ta karbi bakuncin dubunnan daruruwan 'yan kasar Sudan masu neman mafaka da ke zaune a sansanonin da babu kayan amfani yadda ya kamata. Masar da ita me ke fuskantar matsin tattalin arziki, na ta gwagwarmayar karbar 'yan Sudan, inda Sudan ta Kudu ke gaf da hatsarin fada wa sabon rikici, sabod akusancinta da yankunan da ake yin rikicin.

An lalata hanyoyin kasuwanci da ke da muhimmanci ga Gabashin Afirka da Sahel, kuma cibiyoyin kayan amfanin gona irin su El Gezira ma sun lalace, sun kawo matsalar abinci a yankunan. A yayin da ahakan ke faruwa, yadda RSF ke shiga ayyukan fasa-kauri da safarar mutane da makamai, ya sake munana yanayin tsaro a yankin. Idan ba a tsananta bincike ba, Sudan na kan hatsarin zama cibiyar aikata muggan laifuka da za su hana gudanar da shugabanci a lalata tsaro a yankin.

Baya ga munanan ta'annatin da suke aikatawa, mayakan RSF na nuna alamun rauni a cikin gida. Yadda a baya-bayan nan manyan kwamandoji da masu bayar da shwara suka balle na nuni ga samun baraka a rafiyarsu, da kuma tabarbarewar karfin gwiwa a tsakanin manyan mayakan kungiyar.

Sama da mutane miliyan 30 a Sudan na bukatar taimakon jin kai. (Reuters).

A lokaci guda, rundunar sojin Sudan ta mayar da hankali ga kai manyan hare-hare da suka kwato yankuna Khartoum da Sinar masu muhimmanci. Wannan abu ya lalata shirin RSF da yadda suke samun kayan aiki, inda suka koma ga kare kai.

Ga kasashen duniya da ke goyon bayan RSF, wannan cigaba na sanya musu damuwa da kalubale. Cigaba da taimaka wa bangaren da ake ci gaba da yi wa kallon wanda ya gaza marar halasci ba iya rashin nasara ke kawo wa ba, har ma da zubar da mutunci. Karfin RSF da ke dusashewa da yadda ake ware ta dabana na sanya tana kara zama wani nauyi ga masu tallafa mata, wadanda nan da wani lokaci za su fuskanci bacin ran kasa da kasa saboda hannu a ayyukan kisan kiyashi.

Ba a bayar da rahotannin da suka kamata game da rikicin Sudan

Duk da wannan abu da ake gani marar dadi, manyan kafafen yada labarai ba sa dakko rahotanni daga Sudan yadda ya kamata wanda abin damuwa ne matuka, kuma hakan na hana bayar da tallafi yadda ya kamata. Abubuwa da dama ne ke sanya shirun kafafen yada labaran.

Da farko, sauran rikice-rikicen yankuna na jan hankalin kafafen yada labarai na duniya tare da mamaye kanun labarai. Rikicin Ukraine, an dinga bayyana shi a matsayin rikicin kasashen duniya da ke da tasiri na kai tsaye ga Kasashen Yamma, shi ya sa yake mamaye kafafen yada labaran. Haka kuma, rikicin gaza da ake ci gaba da yi na zuwa a shafukan farko na jaridu, saboda yadda yake da dandanon siyasa da tausayi a idanuwan jama'ar duniya. Na baya-bayan nan shi ne rikicin Lebanon da faduwar ba zata da gwamnatin Assad ta yi a Siriya ma sun mamaye kafafen yada labaran. Wani abin mamaki kuma, ana bayyana yakin Sudan a matsayin rikicin yankin da ba shi da wani muhimmanci ga batutuwan siyasa na kasa da kasa.

An rusa kauyuka da dama, an tarwatsa iyalai a yakin na Sudan (AFP).

Batu na biyu shi ne yadda aka hana 'yan jarida samun damar shiga Sudan. An tirsasawa 'yan ajrida da dama barin kasar, sun jefa rayuwarsu cikin hatsari suna neman maboya. RSF da wasu bangarorin na kai wa 'yan jaridu hare-hare, suna hana su motsa wa, tare gaza ba su wata kariya, ana watsi da dokar kasa da kasa da ta ce a dinga kare martabar 'yan jaridu. Kawo rahotanni daga Sudan na da hatsari, inda 'yan jarida ke fuskantar barazana, garkuwa da su da tantancewa mai tsauri. ba sai ma an fada ba, RSF ba su da wani ra'ayi na bayar da dama a sanya idanu kan ayyukan da suke yi, suna ta kawo yanayin da za a yi ta aikata barna a duhu.

A karshe, rashin masu bayar da rahotannin me ke wakana ya gurgunta yadda duniya ke bayar da labarai game da Sudan. 'Yan jaridu na kasahen waje na fuskantar kalubalenshiga kasar. Rikicin da ke kara tsamari da yadda ba a samun damar shiga kasar na kawo nakasun samun cikakkun bayanai na gaskiya. Wannan ya samar da gibin bayanai, wanda ya sanya da wahala a san gaskiyar me ke wakana a kan lokaci, da ma samar da cikakken rahoto.

Wani abu da ke kara ta'azzara wannan yanayi shi ne rikitaccen yanayin rikicin na Sudan, wanda ke kawo babban kalubale ga me kafafen yada ;abarai za su fada. Ba kamar irin yake-yaken da ake iya ganin wa ke kai hari wa ke shan wahala ba, rikicin Sudan ya kunshi wasu masu hannu na yankin, kulla kawance, da wasu abubuwa da suke dakile dakko rahotannin. DUk da haka, mummunan halin da mutane ke ciki na kara ta'azzara, wanda ke kira ga kawo rahotanni na gaskiya da za su bayar da dama a fahimci lamarin.

Kokarin wayar da kan mutane game da Sudan kamar magana ne ga kurame. Babu wanda ya damu da yara kanana da ke cikin yunwa ko kuma wadand aba su ji ba ba su gani ba da RSF ke karkashewa kowacce rana. An manta da Sudan baki daya. Amma ba za mu dakata ba har sai duniya ta ji mu #KuSanyaIdanuKanSudan

Sakamakon da wannan gibi na kafafen yada labarai zai kawo na da muni. Shugabanni da kungiyoyin kasa da kasa na aiki da 'yan bayanai kadan, wanda hakan ke kawo jinkiri ga matakan tallafi da za a su iya dauka don kubutar da rayuka. Gangamin tallafin jin kai, ba ya samun kudaden da suka kamata, inda ake barin miliyoyin mutane babu abinci. A duk lokacin da aka bayar da wani tallafi ba ya isa, inda kashi 32 na dala biliyan 2.7 da MDD ke nema kawai aka iya tattarawa. Kungiyoyin tallafi na bayyana muhimmanci aiki tare da kungiyoyi na cikin gida, saboda babu alamun za a tsagaita wuta a kasar.

Wannan cakudadden yanayi mai muni na kawo tarnaki ga dukkan wani yunkurin kubutar da jama'ar Sudan tare da kawo jinkirin ga duk wani mataki d aake kokarin dauka don warware rikicin.

Kira ga daukar mataki

Kafafen yada labarai na duniya na da muhimmiyar rawar taka wa wajen isar da muruyoyin jama'ar Sudan da yaki ya rutsa da su da kuma sanya wa a tuhumi masu hannu a rikicin. Domin magance wannan gibi na dakko rahotanni, dole ne kafafen yada labarai na kasa da kasa su bayar da fifiko ga yakin Sudan, su zuba jari wajen gudanar da zuzzurfan binciken 'yan jarida da nemo hanyoyi ingantattu na magance kalubalen. Ta hanyar kawo wa duniya halin da Sudan ke ciki, kafafen yada labarai na iya matsa lamba don ganin gwamnatoci, kungiyoyin masu zaman kansu da kungiyoyin agajin jin kai sun yi abinda ya kamata.

Dole ne kasashen duniya su samar da tudun mun tsira don kubutar da 'yan kasar Sudan (AFP).

A lokaci guda, dole ne kasashen duniya su kara karfafa matakin da suke dauka. Samar da tuddan mun tsira don samun damar kai kayan agaji ga yankunan da aka illata, kamar Darfur, fifiko ne da ake bukata cikin gaggawa. Ya kamata kokarin diplomasiyya ya mayar da hankali wajen ganin an tsagaita wuta da kuma goyon bayan matakan da ake dauka don warware rikicin tun daga tushe. Dole ne a karfafa aiki da gaskiya, da suka hada da bincike mai zurfi daga bangaren Kotun Hukunta Manyan Laifuka, domin tabbatar da adalci ga jama'ar Sudan.

Sake zabar Trump na iya ta'azzara kalubalen da rikicin Sudan ke fuskanta. A loakcin mulkinsa na farko, Trump ya rungumi tsarin ba ni in ba ka, tare da samun taimako nan da nan, inda ya kawo sasantawar Sudan da Isra'ila, shi kuma ya cire kasar daga jerin sunayen kasashe 'yan ta'adda.

Sabuwar gwamnatin Trump na iya amfani da wannan salo, ta bayar da fifiko ga bukatu na gajeren lokaci, maimakon warware rikicin baki daya. A yyin da hakan ka iya kawo nasara ta gajeren lokaci da ma tsagaita wuta, tana kuma sanya hatsari saboda togace kokarin kasa da kasa na sake gina Sudan da kuma dakile kokarin neman hakki kan wadanda suka aikata ta'annatin. Ga Sudan, wannan na iya nufin taimako daga kasashen waje da za su bayar da fifiko ga bukatn yankuna maimakon tallafin jin kai, wanda zai kara ta'azzara mummunan halin da ake ciki.

Abdalftah Hamed Ali karamin jami'i ne a Cibiyar Harkokin Duniya ta Gabas ta Tsakiya, yana neman mafita mai dorewa ga gwamutsuwar makamashi, yanayi, da sauyin cigaban al'umma don magance matsalolin yankin na Gabas ta Tsakiya.

Dr. Sahar Khamis kwararriya ce kan kafafen yada labaran Musulmai da Larabawa, inda ta kware wajen rubutu da binciken ilimi. Babbar Jami'a Ba Mazauniya ba a Cibiyar Harkokin Duniya ta Gabas ta Tsakiya, ta zama shugabar Sashen Sadarwa a Jami'ar Qatar kuma Farfesa ce da ta ziyarci Jami'ar Chicago. Ta hada hannu da wasu wajen rubuta litattafai da dama kan batutuwan Musulunci da gwagwarmayar siyasa, kuma yi rubutun litattafai a yarukan Turancin Ilgilishi da Larabci. Dr. Khamis na kuma yin nazari da warwara a kafafen yada labarai, mai jawabi a bainar jama'a. Tana gudanar da wani shirin rediyo a kowanne wata a "US Arab Radio" A lokacin sanyin 2023, an zabe ta a matsayin SHugabar Kungiyar Larabawa Masana Kafafen Yada Labarai Mazauna Amurka.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet