Dollar
35,2631
0.17 %Euro
36,7849
0.16 %Gram Gold
2.967,4600
0.44 %Quarter Gold
4.923,6800
0.00 %Silver
33,7100
0.41 %Mutane da dama a Amurka na ƙaunar jin labaran daukar fansa a fina-finai da kafafan yaaɗ labarai, amma idan aka zo batu na gaske a rayuwa, mafi yawan mu na jan layi - musamman a yanzu haka.
A wajen Amurkawa da dama, "shewa" ga kisan da aka yi na ramuwar gayya ba wai sananniyar al'ada ba ce, masana'anta ce kuma da ke bayar da biliyoyin daloli.
Bayan kisan gillar da aka yi wa Shugaban Zartarwa na Kamfanin UnitedHealthcare, Brian Thompson a farkon watan Disamba, mutane da dama sun yi mamakin me hakan ke nufi inda Amurkawa ke ta daga murya da hargowa kan kisan da aka yi cikin ruwan sanyi babu gaira babu dalili.
Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya-bayan nan da Kwalejin Emerson ta gudanar, a gano cewa mafi yawan masu kaɗa kuri'a (Kashi 68) na tunanin ba za a amince da kisan ba. Sai dai kuma kashi 41 na masu kaɗa ƙuri'ar da ke da shekaru 18 zuwa 29 sun ce kisan "abin amincewa ne" ko "za a iya amincewa da shi."
Wannan na nufi ƙarara cewa mafi yawan Amurkawa ba su amince da kisan a matsayin halayyar da za a amince da ita ba. Mafi yawan mu ba mu amince da kisan gilla na siyasa ba. Amma ɓangaren matasan Amurkawa masu jefa kuri'a na da fahimta sosai kan lamarin.
Tabbas, tun bayan ɓullar kafafan sadarwa na zamani, Amurkawa sun zama masu bayyana me ke cikin zukatansu da biris da me mutane za su ce inda har suke murna idan aka aikata wani mummunan abu kan wani babba ko mashahuri.
Yaushe ne halayya a baki ko a kafar yada labarai don murnar ganin wani rikici, a fim ko a gaske, ya rikiɗe zuwa zama rikicin gaba da gaba?
Tabbas, wani bangare na matasan Amurkawa na murna ga wanda ya yi kisan tare da yaba hanyoyin da ya bi na taso da batun kamfanonin kula da lafiya. To me zai faru idan aka samu sauyin manufa?
Koken karfin iko
Da farko, yana da muhimmanci a bambance tsakanin hatsarin rikici na gaske da kuma zantuttukan 'yan siyaa, da kuma masu tallata kayayyaki da masu karfin fada a ji.
Idan aka kalli zanga-zangar da aka yi a Majalisar Dokokin Amurka a ranar 6 ga Janairu, 2021. Wadannan al'amura na nuni da cewa wani bangare na Ƙasashen Yamma ya yi murna da ma ingiza afkuwar rikicin.
A yayin da karɓar wannan ke iya zama sabon abu, za kuma mu iya kallon sake zabar Shugaba Donald Trump bayan zanga-zangar Capitol ko goyon bayan ƙasa ga Firaministan Isra'ila a matsayun hujjar rikicin kansa wanda za a iya amince wa da shi a yau.
Amma shin wannan goyon baya na nuni ga bukatar goyon bayan samun irin wannan rikici, ko kuma wata bukata ce ta hambarar da tsarin da mutane da dama ke wa kallon marar kyau ko mai kawo asarar rayuka? Tabbas, batun rikici da hayaniya ya zama wani bangare na nuna goyon bayan siyasa da biyan bukatar manufa.
Kenan wasu daga cikinmu sun zama masu bayyana ra'ayinsu ƙarara ko suna jin kunyar yabon masu aikata ta'annati waɗanda suke cewar sun ɗauki fansa ne - amma fa sai a lokacin da muka yarda da su.
Amma me ya sa? To, ka taba jin labarin Bruce Wayne (Batman) ko John Wick, mai kisan gillar da Keanu Reeves ya fito a matsayinsa a shirin fim? ko ma Beatrix "amaryar nan" Kiddo, Uma Thurman ta cikin shiri mai dogon zango na 'Kill Bill'?
Tun bayan harin 11 ga Satumban 2001, an samu sauyi sosai a fagen kafafen yada labarai na gargajiya sama da na yanar gizo, kuma wannan na bukatar a bayyana shi. Gaskiyar ita ce, masana'antar Hollywood cike ta ke da jaruman da suka kware wajen daukar fansar kisa, da kuma labaran fim irin haka da suka mamaye al'adunmu.
A lokacin da Amurkawa ke adawa da duk wasu matsaloli na zamantakewa da siyasa, amma abu ɗaya da har yanzu ba su nuna adawa da shi ba shi ne daukar fansa ko ramuwar gayya. Tabbas, da yawan mu na koma wa gida cikin iyali su fara kallon abin da za a iya kira kawai na ban sha'awa da kisa mummuna na "waɗanda suka yi mana laifi".
Misali, manyan fina-finan 2024 da suka yi shuhura sun hada da Dune 2, Deadpool da Wolverine, sai kuma shirin Bad Boys, wanda duk suke ɗauke da manyan rikici.
A saboda haka, ta wasu hanyoyin, ɗaukar fansa na iya zama kasuwanci mai kawo riba ga masana'antar da ke nishaɗantarwa. Wasannin bidiyo da wasannin kai tsaye na taka rawa, fina-finai da sauran nau'ikan nishadi na nuna yadda ɗaukar fansa ta zama gama-gari a matsayin abin neman kawar da damuwa.
Kuma kafafan sadarwa na zamani na ƙara ingizawa da nuna goyon bayan ɗaukar fansar, kuma a yanzu batu ake na kisan gilla na siyasa.
Sakamako kan al'umma
Amurkawa mutane da aka sani da naɗe hannu suna kallon ana cin mutunci ko fuskar mutumin da ake ɗaukar fansa a kansa. Kai ta kai ma a ce kowa na zama cikin farin ciki bayan hakan, haka ne?
Mutumin da ake zargi da kashe babban jami'in kamfanoni, da ya yi karatu a Ivy League, Luigi Mangione, na iya fuskantar hukuncin kisa, saboda a yanzu kotun tarayya na tuhumar sa da aikata babban laifi, sannan jiha na tuhumar sa da ta'addanci, duba ga abinda ya faɗa a bayaninsa.
Duk abubuwan da aka faɗa, ba za a musanta cewa mu Amurkawa muna shaida afkuwar faɗa da kisa a koyaushe.
A yanzu yaƙe-yaƙe ma ana watsa su a talabijin da wayoyin hannunmu a gidajenmu. Ba za a iya musanta cewa hare-haren bindiga a yau na ta ƙaruwa ne a Amurka. masu neman damar yaki na kan sahun gaba a duniya a yau.
Sannan akwai batun tsoro.
A watan Disamba, Daraktan FBI Christopher Wray ya bayar da shaida a gaban kwamitin shari'a na majalisar dattawa. An tambaye shi ko ya ga "alamun akwai matsala?" - ana maganar alamun gargadi ga Amurka kafin a kai harin 11 ga Satumba.
Wray ya bayar da amsa da cewa "Na dinga ganin alamun matsala a duk inda na waiwaya," yana mai cewa ya damu game da hare-haren kamar yadda aka damu da harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a watan Oktoba.
Ana amfani da kafafan yaɗa labarai. Amma waɗannan munanan hare-hare ba su taɓa zama abin so ba. Kai hasali ma, ba a ma taaɓ samun wani rikici mummuna ba a lokacin zaɓen Amurka - sai dai- ɓacin ran jama'a da yunƙurin kisan gillar da ba a yi nasara ba.
Kazalika, irin rikicin da Amurkawa ke yin murna idan an aikata, da ma can an san yaya suke.
To Amurkawa nawa ne ke goyon bayan kisan gilla? Kuma shin ƙaruwar da aka samu a baya-bayan nan na da muhimmanci wajen sauya tunani da halayenmu?
Shirye-Shiryen labarai da nishadantarwa da ake yaɗa wa awanni 24 ba sa iya gamsar da al'ummarmu da ba su abubuwan da suke so, aƙalla a ce kamar yadda yake ɗauke a cikin kundin halayyar rikici.
Haka kuma, kafafan sadarwa na yanar gizo da gidajen jaridu masu yaɗa shiri tsawon awanni 24, sun zama masu kambama wa da karin gishiri a miya da ma kukuza wanda suka fi magana a tsakaninmu.
Tattaunawa, tsana da rashin bin ka'ida na ta daduwa sakamakon danna rubutun yanar gizo da dade wa ana kallon talabijin ko waya. bari mu hadi me jaridar yore ke cewa, idan jini ya fita, sai ya zama a kan gaba.
Amma nawa ne za su ɗauki mataki?
Wataƙila 'yan kaɗan a yanzu. Babu wani da ya gudanar da wani taro ko hargowa da za a iya kallo a matsayin abin da ya sanya mai kisan kan aikata laifin.
Lokaci ne zai bayyana ko mashahurinmu zai samu karɓuwa da maraba daga masu kisan kai ko masu irin tunaninsa na yin kisa a nan gaba, wanda muke kallo a al'adun matasa na harbe-harbe da ta'addanci.
Kusan za a ce babu wani abu da ya wuce kalmomin yabo da jinjinawa. Idan kuma aka zo batun karfin faɗa-a-ji da jan ra'ayi, sai a dinga bayyana neman sauya ɗabi'u a matsayin jigon gangamin neman ƙarfi da ya yi nasara.
A nan gaba zan fito na bayyana babu wani mahaluƙi a Amurka da zai ɗauki makami ya ɗauki fansa kamar yadda makashin shugaban kamfanin ya yi. Wasu za su ci gaba da yin zambo da shagube ga tsarin kula da lafiya na Amurka, wasu 'yan tsiraru kuma za su yi ƙoƙarin aikata kisan gilla.
Ko da ace wannan ɗan ƙaramin rukici na Amurkawa ya amince da irin waɗannan laifuka, gaskiyar zance shi ne mafi yawan jama'a ba sa goyon bayan a dinga aikata kisan gilla.
Akwai 'yan alamun rikici daga hargowar da muke ji muke kallo a talabijin da wayoyin hannu. Wataƙila hakan sauƙin ka nade hannu ka yi ta kallo ne da kuma amayar da ɓacin rai?
A yayin da muke sauraren ganin afkuwar rikici, babu wani daga cikin murnar aikata laifukan da ke da amfani.
Marubucin wannan maƙala, Dr Matthew Schumacher Daraktan Asibiti kuma Babban Mai Bincike a ƙungiyar 'Oaretnts 4 Peace, Masanin Halayyar Tsaro ta Kasa da kuma tsohon mayakin GWOT, Tsohon Laftanal Kwamanda, kuma Farfesa a fannin likitancin ƙwaƙwalwa a Rundunar Sojin Ruwan Amurka. Ya yi kusan shekaru 20 a aikin soja kuma ya mayar da hankali kan halayyar ɗan'adam da shugabanci inda ya je Iraki da Afirka da Afganistan don tallafa wa sojoji. Ƙwararre ne a soji da sanin tsaron ƙasa, da magance matsalar ƙwaƙwalwa da buƙatar gaggawa ta masu taɓin hankali, kuma yana da kwarewa wajen koyar da likitoci.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.
Comment