Tokyo: 07:02 AM
Londra: 10:02 PM
New York: 05:02 PM
İstanbul: 01:02 AM

Dollar

38,2552

0.34 %

Euro

43,8333

0.15 %

Gram Gold

4.076,2000

0.31 %

Quarter Gold

6.772,5700

0.78 %

Silver

39,9100

0.36 %

Aljeriya ta bayyana cewa “ya zama dole mu rama” bayan Mali da Nijar da Burkina Faso sun yi wa jakadunsu kiranye daga babban birnin ƙasar Algiers.

Algeria ta hana Mali amfani da sararin samaniyarta

Aljeriya ta rufe sararin samaniyarta ga Mali tare da yi wa jakadanta kiranye daga ƙasar sakamakon ce-ce-ku-ce game da zargin kakkaɓo jirgin sama mara matuƙi na Mali a maƙwabciyarta.

"Saboda keta dokokin sararin samaniyarmu da ƙasar Mali ke yi a-kai-a-kai, gwamnatin Aljeriya ta yanke hukuncin hana zirga-zirgar jirage da ke tahowa ko tafiya Mali daga yau," kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Aljeriya ta faɗa ranar Litinin.

Algiers ta kuma yi wa jakadanta zuwa Nijar kiranye a wani mataki na ramuwar gayya bayan ƙasashen biyu tare da Burkina Faso sun yi wa jakadunsu kiranye kan zargin kakkaɓo jirgin na Mali.

Ƙawancen ƙasashen ukun da sojoji ke mulka ya yi wa jakadunsu kiranye ranar Lahadi. Mali ta zargi Aljeriya da kakkaɓo ɗaya daga cikin jiragenta mara matuƙa a cikin ƙasarta a makon da ya gabata, zargin da Aljeriya ta musanta.

Arewacin Mali na da kan iyaka da Aljeriya kuma nan ne ‘yan tawaye masu son a raba ƙasar ke yaƙi yayin da hare-haren ‘yan ta’adda ke ci gaba da addabar ƙasar.

’Zarge-zarge mara tushe’

Ranar Litinin Aljeriya ta bayyana "cewa ya zama dole mu rama " bayan matakin da ƙasashen uku suka ɗauka.

A wani ɓangare na matakin, sabon jakadan Aljeriya zuwa Burkina Faso zai jinkirta kama aiki, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Aljeriya ta bayyana a wata sanarwa.

 "Zarge-zargen mara tushe ", da ke zuwa musamman daga Mali, " sun kasa ɓoye neman mafita da kuma raba hankali daga gazawa da ta bayyana ƙarara na aikin ‘yan juyin mulki, lamarin da ya tsunduma Mali cikin guguwar rashin tsaro da rashin zaman lafiya da tashin hankali da fatara," in ji ta.

A ranar ɗaya ga watan Afrilu dai Aljeriya ta ce ta kakkaɓo wani jirgi mara matuƙi mai makami da ke tattara bayanai a sararin samaniyarta ba tare da ta bayar da ƙarin bayani ba.

Nijar da Burkina Faso da Mali sun ƙafa ƙungiyar tarayyarsu ta ƙasashen Sahel (AES), wadda aka kafa daga farko a matsayin yarjejeniyar tsaro a shekarar 2023.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#