Sport
Dollar
38,2552
0.34 %Euro
43,8333
0.15 %Gram Gold
4.076,2000
0.31 %Quarter Gold
6.772,5700
0.78 %Silver
39,9100
0.36 %Shugaban Nijar Abdourahmane Tiani ya yi garambawul ga gwamnatinsa inda ya ƙara yawan ministocinsa daga 23 zuwa 26 tare da naɗa sabbin ministoci takwas.
Shugaban kasar Nijar, Janar Abdourahmane Tiani, ya yi wani gagarumin sauyi ga gwamnatinsa a ranar Alhamis, 17 ga watan Afrilu, inda ya faɗaɗa majalisar ministocinsa zuwa mambobi 26, idan aka kwatanta da 23 a baya.
Waɗannan muhimman sauye-sauyen, waɗanda suka ƙunshi samar da sabbin ma’aikatu uku da kuma yin garambawul a ofisoshi da dama, ya haifar da naɗa sabbin ministoci takwas, ciki har da mambobin kwamitin da ya gudanar da taron ƙasa.
Daga cikinsu akwai Abdoulaye Seydou, wanda shi ne jagoran tafiyar M62, wanda a halin yanzu shi ne Ministan Kasuwanci da Masana’antu.
Haka kuma Ali Ben Sala Hamouda an ƙara masa girma zuwa Ministan Al’adu da Inganta Ɗabi’un Zamantakewa. Ta ɓangaren waɗanda za su bar muƙaminsu, Ms Aïssa Laouan Wandarama da kuma Mista Mohamed Sidi Raliou, za su ba muƙaminsu.
Sabbin ministocin da suka samu gurbi a gwamnatin Janar Tiani sun haɗa da Kanal Abdoulkadri Amadou Daouda wanda ya karɓi ragamar Ma’aikatar Tsara Birane da Gidaje, sai Abdoulaye Seydou, wanda shi ne jagoran tafiyar M62 inda ya zama Ministan Kasuwanci da Masana’antu.
Haka kuma Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta faɗa kan Sidi Mohamed Al Mahmoud, sai kuma Ali Ben Sala Hamouda ya zama Ministan Al’adu da Inganta Ɗabi’un Zamantakewa.
Haka kuma malaman jami’o’i biyu masu muƙamin farfesa biyu sun zama ministoci.
Sun haɗa da Sidikou Ramatou Djermokoye Seyni wanda aka bai wa Ministan Ƙidaya da Farfesa Farmo Moumouni wanda ya zama Ministan Ilimi da Koyar da Sana’o’i.
Haka kuma Adji Ali Salatou shi ne sabon Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani.
Sai kuma Mahamane Sidi ya zama wakilin firaminista wanda zai mayar da hankali kan kasafin kuɗi.
Comments
No comments Yet
Comment