Dollar

35,4691

-0.04 %

Euro

36,6653

0.20 %

Gram Gold

3.058,1400

0.16 %

Quarter Gold

5.028,7800

0.82 %

Silver

34,5800

1.36 %

''Za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen tallafawa ayyukan samar da wutar lantarki a yankunan karkara na bankin duniya, inda aka ware dala miliyan 50 domin bunkasa hanyoyin sabunta makamashi'' a cewar Fagbemi.

Amurka ta mayar wa Nijeriya $52.88m na kadarorin kasar da 'Diezani ta karkatar'

Amurka ta mayar wa gwamnatin tarayyar Nijeriya dala miliyan 52.88 na wasu kadarorin da aka kwato daga cikin wadanda tsohuwar ministar man fetur ɗin ƙasar Diezani Alison-Madueke ta karkatar daga ƙasar.

Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard M. Mills, Jr ne ya jagoranci tawagar ƙasar da ta sa hannu kan yarjejeniyar maido da kadarorin a hedikwatar ma’aikatar shari’a ta tarayya da ke Abuja, ranar Juma’a.

Babban lauya tarayya kana minsitan shari'a a Nijeriya Lateef Fagbemi wanda ya wakilci gwamnatin Nijeriya ya ce kudin da aka maido an same su daga kadarorin kamfanin Galactica Star da ke da alaka da tsohuwar Ministar da mukarrabanta.

A cewar ministan, wannan ci gaban da aka samu ba kawai nuna iya ƙoƙarin da kuma jajircewar kasashen biyu wajen yaki da ayyukan cin hanci da rashawa ba, har da nuna ƙudurin Amurka na maido da kadarorin da aka sace da kuma martaba hanyoyin gaskiya da riƙon amana a harkokin mulki.

''Za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen tallafawa ayyukan samar da wutar lantarki a yankunan karkara na bankin duniya, inda aka ware dala miliyan 50 domin bunkasa hanyoyin sabunta makamashi'' a cewar Fagbemi.

Ragowar dala miliyan 2.88 kuma Nijeriya za ta bayar da su ne a matsayin tallafi ga cibiyar shari’a ta kasa da kasa don tallafa wa ayyukan yaki da ta’addanci a fadin Afirka, in ji shi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#