Dollar

38,2552

0.34 %

Euro

43,8333

0.15 %

Gram Gold

4.076,2000

0.31 %

Quarter Gold

6.772,5700

0.78 %

Silver

39,9100

0.36 %

Wasu bayanai da aka riƙa yaɗawa a shafukan intanet sun yi iƙirarin cewa Babban Bankin Nijeriya (CBN) zai ƙaddamar da sabbin takardun kuɗi na N5,000 da N10,000 a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2025.

CBN ya musanta fitar da sabbin takardun kuɗi na N5,000 da N10,000

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaryata wasu rahotanni da ke cewa yana shirin ƙaddamar da sabbin takardu kuɗi na N5,000 da N10,000.

CBN ya ce sanarwar da aka yi ta yada wa ta kafar WhatsApp, wacce aka danganta shi da ita wanda ke cewa “Babban Bankin Nijeriya (CBN) a hukumance na sanar da samar da sabbin takardun Naira guda biyu – N5,000 da N10,000, a matsayin wani bangare na kokarin daidaita hada-hadar kudi da inganta harkokin kudi a Nijeriya.” babu gaskiya a ciki.

Kazalika sanarwar ta yi ikirarin cewa daya daga cikin mataimakin gwamnan babban bankin CBN, Dr. Ibrahim Tahir Jr., ne ya tabbatar da yunkurin a matsayin wani mataki na rage yawan kudaden da ake kashewa wajen hada-hadar kudi tare da baiwa ‘yan Nijeriya zabuka masu inganci a hada-hadar kasuwanci.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#