Dollar

38,2552

0.34 %

Euro

43,8333

0.15 %

Gram Gold

4.076,2000

0.31 %

Quarter Gold

6.772,5700

0.78 %

Silver

39,9100

0.36 %

Mataimakin ministan kuɗin Ghana, Mista Thomas Nyarko Ampem ya bayyan sauƙin da soke dokar harajin zai kawo wa ‘yan ƙasar, inda ya ce matakin zai sa a mayar wa ‘yan Ghana cedi biliyan biyu ( kimanin naira biliyan 198).

Majalisar Dokokin Ghana ta soke dokar harajin tura kuɗi ta intanet

Majalisar Dokokin Ghana ta soke dokar harajin tura kuɗi ta intanet ranar Laraba.

Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ruwaito cewa dokar harajin tura kuɗin da aka fi sani da E-Levy wadda ta fara aiki a shekarar 2022 ta ƙaƙaba harajin kashi ɗaya cikin ɗari kan kuɗin da ake turawa ta waya ko ta banki ko kuma aka karɓa daga ƙetare.

Ana sa ran soke dokar harajin zai sauƙaƙa wa ‘yan ƙasar matsin tattalin arziki da suke fama da shi tare da haɓaka kasuwanci a intanet.

A baya dai dokar harajin tura kuɗin ta fuskanci adawa mai yawa daga gama-garin mutane da masu ruwa da tsaki, waɗanda suka ce dokar ta ƙara nauyi kan ‘yan ƙasar tare da hana mutane amfani da intanet wajen hada-hadar kuɗi.

Mataimakin ministan kuɗin Ghana, Mista Thomas Nyarko Ampem ya bayyan sauƙin da soke dokar harajin zai kawo wa ‘yan ƙasar, inda ya ce matakin zai sa a mayar wa ‘yan Ghana cedi biliyan biyu ( kimanin naira biliyan 198).

“Ya shugaban majalisa, soke dokar E-Levy zai mayar wa mutane cedi biliyan biyu, lamarin da zai sauƙaƙa wa mutane nauyin kuɗi tare da inganta rayuwarsu,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ambato mataimakin ministan yana cewa.

Soke dokar harajin na E-Levy ya dace da ƙoƙarin gwamnatin ƙasar na inganta yawan mutane da ke cikin tsarin kuɗin ƙasar tare da ƙarfafa gwiwar mutane wajen amfani da hanyoyin tura kuɗi ta intanet ba tare da ƙaƙaba wa mutane haraji ba.

‘Yan kasuwa da yawa da ma’aikatan kamfanonin tura kuɗi  da masu sharfi kan lamaruan kuɗin sun soki harajin a baya inda suka bayyana tasirinta kan hada-hadar kuɗi ta intanet da  kuma samun damar gudanar da hada-hadar kuɗi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#