Sport
Dollar
38,0464
-0.23 %Euro
43,5203
-0.57 %Gram Gold
4.061,5200
-0.91 %Quarter Gold
6.720,2300
-0.17 %Silver
39,7700
-1.02 %Shugaban Turkiyya ya nuna fatan kyakkyawar alaƙa cike da taka-tsantsan dangane da alaƙar Turkiyya da Amurka, yana cewa Ankara tana sha’awar ganin matakai na zahiri sun biyo bayan kalamai, musamman a ɓangaren haɗin gwiwar tattalin arziki.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da cewa ba a sanya wata rana ba domin yiwuwar ziyara zuwa Amurka, amma ya nuna ci-gaba da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu, musamman kan al'amuran tattalin arziki kamar ka'idojin haraji.
Da yake magana da ‘yan jarida a Istanbul ranar Juma’a, Erdogan ya bayyana cewa ba a kammala tsayar da lokaci ba kan yiwuwar ziyarar zuwa Washington.
“Ba a kammala tantance ainihin lokacin da ɓangagren Turkiyya zai kai ziyarar aiki zuwa Amurka ba,” kamar yadda ya bayyana.
Duk da cewa akwai rashin tabbbas, Erdgogan ya nuna cewa za a ci gaba ta ttaunawa a matakin ministoci tsakanin ƙasashen biyu.
“Duk da haka, a halin da ake ciki, ministana na harkokin ƙasashen waje (Hakan Fidan) da ministan cinikayya (Omer Bolat) zai iya kasancewa suna da tsare-tsaren tattaunawa ko shirin tafiye-tafiye da ke da alaƙa da Amurka,” kamar yadda bayyana.
Erdogan ya ƙara da cewa waɗannan tattaunawar za su taɓa “batutuwan da suka shafi ƙa’idojin harajin da aka ƙara a baya bayan nan,” abin da Ankara take gani a matsayin wani mataki na ƙarfafa alaƙar tattalin arziki da Washington.
Ya nuna fata mai kyau mai cike da taka tsantsan game da halin da ake ciki yanzu a dangantakar Amurka da Turkiyya.
“Muna fatan ganin kyakkyawan yanayin da suke la'akari da shi ga Turkiyya ya zama aiki na zahiri,” in ji Erdogan, yana nuna sha'awar Ankara ta ganin matakai na zahiri sun biyo bayan kalamai, musamman a ɓangaren haɗin gwiwar tattalin arziki.
Wani ‘sabon zamani’ a alaƙar diflomasiyya
Kalaman sun biyo bayan tattaunawa ta waya a ranar 16 ga Maris tsakanin Erdogan da Shugaban Amurka Donald Trump, inda Erdogan ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa Turkiyya da Amurka za su ƙara ƙarfafa dangantaka. A lokacin wannan tattaunawar, Erdogan ya jaddada yiwuwar ci gaba da haɗin gwiwar ƙasashen biyu ta hanyar “haɗin kai, da hanyar da za a samu sakamako mai ma’ana, da kuma amana.”
Duk da cewa dangantaka tsakanin Ankara da Washington ta kasance cikin yanayi mai tsauri a wasu lokuta a 'yan shekarun nan — saboda rashin jituwa kan goyon bayan Amurka ga ƙungiyar 'yan ta'adda ta PKK/YPG, da sayen kayan tsaro, da rikice-rikicen yankin — ɓangarorin biyu sun nuna sha'awar sake saita yanayin. Ana ganin tattaunawar da ake yi da kuma yiwuwar ziyarar manyan ministocin Turkiyya a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ci gaba da tattaunawar tsakanin ƙasashen biyu.
Kamalan na Erdogan sun zo ne a lokacin da Turkiyya ke neman janyo ƙarin zuba jari daga waje, da kuma warware batutuwan cinikayya da ake da su da manyan abokan hulɗa, ciki har da Amurka.
Tsare-tsaren haraji da dokoki na daga wani ɓangare na tattaunawar da ake ci gaba da yi don share hanyar haɗakar tattalin arziki mai ma’ana.
Comments
No comments Yet
Comment