Dollar

38,1219

0.08 %

Euro

43,4706

0.93 %

Gram Gold

4.004,8500

1.25 %

Quarter Gold

6.511,6500

0 %

Silver

39,6300

0.08 %

Erdogan ya yi alkawarin ci gaba da haɗin kai da gwamnatin Siriya don kare haɗin kan ƙasar, da hana ƙoƙarin tayar da hankalin ƙasar daga waje, da adawa da ƙoƙarin mayar da hannun agogo baya kan ci-gaban da ake samu tun daga ranar 8 ga Disamba.

Erdogan: Wadanda suke hana zaman lafiya a Syria za su fuskanci Turkiya da Damascus tare

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi gargaɗi mai ƙarfi kan batun Siriya, yana mai jaddada cewa Turkiyya za ta tsaya tsayin daka tare da gwamnatin Siriya wajen kare yankin ƙasar da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Da yake magana da manema labarai bayan taron Majalisar Ministoci a ranar Talata, Shugaba Erdogan ya sake tabbatar da goyon bayan Turkiyya ga ikon cin gashin kan Siriya da kwanciyar hankalinta, yana kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a rikicin da su yi halin dattako.

“Duk wanda ya yi ƙoƙarin hana Siriya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa,” in ji Erdogan, “za su tarar da Turkiyya tare da gwamnatin Siriya suna tsayin daka a gabansu.”

Adawa da sabuwar rabuwar kai

Erdogan ya bayyana a fili cewa Ankara ba za ta amince da kowanne yunƙuri na raba kan Siriya ba, ko da a ƙarƙashin wata dabara ce.

Da yake magana kan ƙoƙarin wasu ƙungiyoyi a baya na ƙirƙirar abin da ake kira “farfajiyar ta’addanci” a kan iyakar kudancin Turkiyya, ya ce: “Kamar yadda ba mu bari an raba Siriya ta hanyar farfajiyar ta’addanci ba, ba za mu bari a raba ta ta kowacce hanya ba.”

Wannan magana ta nuna tsokaci kan hare-haren Isra’ila a Siriya da kuma adawar da Turkiyya ke yi ga ‘yan ta’addan YPG/PKK da Amurka ke mara wa baya a arewacin Siriya, waɗanda suke reshe ne na ƙungiyar ta’addanci ta PKK.

‘Babu komawa baya’ bayan 8 ga Disamba

Da yake jaddada muhimmancin abubuwan da suka faru kwanan nan a Siriya, Erdogan ya bayyana cewa yanayin siyasa da na soja kafin 8 ga Disamba ba shi da amfani a yanzu.

“Babu yiwuwar dawowa ga yanayin da ake ciki kafin 8 ga Disamba,” in ji shi, yana nuni da abin da ya kira “juyin juya hali na 8 ga Disamba” — alamar sabon zamani a harkokin cikin gida na Siriya da diflomasiyar yankin. “Sabon mataki ya fara a ƙasar tare da juyin juya hali na 8 ga Disamba.”

Saƙo ga ƙasashen waje

A cikin wata magana da aka ɗauka a matsayin saƙo ga masu ruwa da tsaki na duniya da ke cikin harkar Siriya, shugaban Turkiyya ya ce wasu ƙasashe ya kamata su daina gwada haƙurin Turkiyya kuma su gane darajar abokantakarta.

“Maimakon gwada iyakar Turkiyya dangane da Siriya,” ya gargadi, “ya kamata wasu ƙasashe su darajta abotarmu kuma su yi aiki kamar ƙasa — ba kamar wata ƙungiya ba.”

Ana fassara wannan magana a matsayin wata suka kai-tsaye ga ƙasashen da ke goyon bayan ƙungiyoyi marasa tsari ko ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a Siriya ba tare da haɗin kai da ƙasashen yankin kamar Turkiyya ba, wacce ta gudanar da ayyuka da dama na tsallake iyaka don tabbatar da tsaron ƙasa.

A cikin watannin baya-bayan nan, Turkiyya ta bayyana goyon bayanta ga haɗin kan Siriya tare da jaddada buƙatar samun mafita ta siyasa da za ta tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#