Dollar

38,2552

0.34 %

Euro

43,8333

0.15 %

Gram Gold

4.076,2000

0.31 %

Quarter Gold

6.772,5700

0.78 %

Silver

39,9100

0.36 %

Rahotanni sun ce fursunonin sun yi musayar wuta da masu gadi a lokacin da wani gwamnan jiha ya kai musu ziyara inda har suka jikkata gwamnan.

Fursunoni fiye da 100 sun tsere daga gidan yari a Chadi

Fursunoni fiye da 100 sun tsere daga wani gidan yari a Chadi a yayin musayar wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku da jikkata gwamnan jiha a lokacin da ya kai ziyara gidan fursunan, kamar yadda hukumomi suka tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sun tsere ne a ranar Juma’a da maraice a yayin wani rikici da ya ɓarke a gidan yarin mai nisan kilomit biyar daga garin Mongo da ke tsakiyar ƙasar.

“Akwai kusan 100 da suka tsere, uku sun mutu, uku kuma suka jikkata in ji Hassan Souleymane Adam, babban sakataren lardin Guera da Mongo ke cikinta.

Wani jami’in yankin Mongo ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa fursunonin sun kutsa cikin ofishin manaja domin satar bindigogi.

“An yi artabu da masu gadi, a daidai lokacin da gwamnan ya iso, ya samu rauni,” inji shi.

Jami'in na Mongo ya tabbatar da mutuwar mutane uku, ya kuma ce adadin fursunonin da suka tsere ya kai 132.

Ya ce fursunonin sun tayar da tarzoma ne bayan sun koka kan rashin abinci.

Ministan shari’a na Chadi Youssouf Tom ya ce zai hau jirgi ya je yankin kuma zai bayar da bayani kan cikakken abin da ya faru.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#