Dollar

37,9525

0.01 %

Euro

42,0657

1.98 %

Gram Gold

3.792,7600

-0.89 %

Quarter Gold

6.304,8300

-0.43 %

Silver

38,9800

-5.93 %

An kama ministocin ne bayan da sojoji suka ƙwace mulki kana suka tsare su a gidajen yari daban-daban.

Gwamnatin Nijar ta saki ministocin gwamnatin Bazoum da aka hamɓarar

Gwamnatin Nijar ta saki kusan mutane 50 da suka haɗa da ministoci da aka tsare tun bayan da sojoji suka ƙwace mulki daga gwamnatin farar hula ta Bazoum a watan Yulin 2023.

Waɗanda aka saki sun haɗa da tsofaffin ministoci da jami’in diflomasiyya da wani ɗan jarida da kuma wasu sojoji da ake zarginsu da yunƙurin juyin mulki a shekarar 2010. Sai dai har yanzu ana ci gaba da tsare hamɓararren tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

“An sako waɗannan mutane ne bisa ga shawarwarin da ƙungiyar sake gina ƙasar ta bayar,” a cewar babban ofishin sakatariya na gwamnatin Nijar a cikin wata sanarwa da aka karanta ta gidan talabijin ɗin gwamnatin ƙasar.

Cikin mutanen da aka saki har da tsohon ministan man fetur Mahamane Sani Issoufou, ɗan tsohon shugaban ƙasa Mahamadou Issoufou wanda ya shafe shekaru goma a kan mulki tun daga 2011, da kuma tsohon ministan tsaro Kalla Moutari, da tsohon ministan kuɗi Ahmat Jidoud, da kuma tsohon ministan makamashi Ibrahim Yacoubou.

Afuwa da sulhu

Shugaban jam'iyyar PNDS wadda ta taɓa yin mulki, Foumakoye Gado da ɗan jarida Ousmane Toudou suma suna cikin waɗanda aka sako tare da Alat Mogaskia, tsohon jakadan Nijar a Nijeriya.

Ana dai ci gaba da tsare tsohon shugaban ƙasar Bazoum, wanda yake fuskantar tuhume-tuhume da dama, kana an janyar kariyar da yake da ita ba tare da an sanya ranar shari'a ba.

An kuma saki sojojin da a baya aka samu da laifin yunƙurin juyin mulki da kuma janyo "barazana ga tsaron kasar", ciki har da Janar Salou Souleymane, da tsohon babban hafsan hafsoshin sojin ƙasar, da wasu jami'ai uku da aka yankewa hukuncin daurin shekaru 15 a shekarar 2018 a gidan yari, saboda ƙoƙarin hamɓarar da Shugaba Issoufou a shekarar 2015.

Taron ƙasa da aka gudanar a watan Fabrairu ya ƙarfafa wa gwamnatin mulkin sojin Nijar gwiwa ta hanyar baiwa Tiani izinin ci gaba da mulki a kasar na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

"Ina so in sake jaddada aniyata na yin aiki tukuru don yin afuwa da sulhu a tsakanin 'yan Nijar," in ji shugaban Tiani bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a makon jiya.

"Yin afuwa da sulhu da muke kira a kai ba zai ci karo da halaltaccen muradin 'yan Nijar na yin adalci ba."

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#