Sport
Dollar
38,0406
0.24 %Euro
41,9406
-0.47 %Gram Gold
3.694,2100
-2.7 %Quarter Gold
6.293,2300
-0.18 %Silver
36,3700
-6.4 %Wata majiyar tsaro ta ce "an kashe 'yan bindiga da yawa a wani mataki na mayar da martani".
Wasu mutane da ake zargi ‘yan bindiga ne sun kashe sojoji da fararen-hula da dama a hare-haren da suka kai a gabashin Burkina Faso, kamar yadda mazauna yankin da kuma jami’an tsaro suka tabbatar ranar Lahadi.
Wata majiyar tsaro a lardin Tapoa ta shaida wa kamfanin dillancn labarai na AFP cewa ‘yan bindiga sun kai “mummunan hari” kan wasu rukunin sojoji a birnin Diapaga ranar Juma’a. Mutanen da suka kashe sun haɗa da sojoji da ‘yan-ƙato-da-gora da ke taya su yaƙi da masu tayar da ƙayar baya, sannan an jikkata mutane da dama.
Kazalika wata majiyar tsaro ta daban ta tabbatar da kai harin, sai dai ta ƙara da cewa an kashe ‘yan bindiga da dama a wani mataki na mayar da martani kuma sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari a yankin.
Wasu majiyoyi daga asibitin birnin Fada N'Gourma da ke gabashin yankin sun ce, "kusan mutum 30 ne suka jikkata, dukkansu jami’an tsaro, inda aka kwashe su ranar Asabar" zuwa asibitin.
Tun shekarar 2015 Burkina Faso take fama da rikicin masu tayar da ƙayar baya da ke da alaka da ƙungiyoyin Daesh da Al Qaeda.
Rikicin ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 26,000, a cewar cibiyar ACLED wadda ke tattara bayanai game da rashin tsaron da ke addabar ƙasar, sannan fiye da mutum miliyan biyu sun tsere daga gidajensu sakamakon rikicin.
Comments
No comments Yet
Comment