Dollar

35,5082

0.07 %

Euro

36,5801

-0.05 %

Gram Gold

3.061,3600

0.26 %

Quarter Gold

4.987,7800

0.00 %

Silver

34,2000

0.24 %

Kisan kare dangi na Isra'ila a Gaza - wanda ke cikin kwanaki 466 - ya kashe Falasdinawa sama da 46,584 tare da jikkata wasu 109,731. A Lebanon, Isra'ila ta kashe akalla mutane 4,063 tun daga watan Oktoban 2023.

Isra'ilawa 11 sun jikkata sakamakon harin makami mai linzami na Houthi

Talata 14 ga Janairun 2025

0700 GMT — Isra'ilawa 11 sun jikkata sakamakon harin makami mai linzami na Houthi

Akalla Isra’ilawa 11 ne samu raunuka yayin da suke ƙoƙarin tsira bayan da makami mai linzamin da aka harba daga Yemen ya nufi tsakiyar Isra’ila, a cewar kafar yada labaran Isra’ila KAN.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarun tsaronta na sama sun daƙile harin makamin kafin ya shiga sararin samaniyar Isra'ila.

An yi ta jin ƙarar jiniya ta sama a tsakiyar Isra'ila, lamarin da ya sa dubban mutane neman mafaka.

Tawagar likitocin sun bai wa mutum 11 agaji da suka samu raunuka yayin da suke gudu zuwa matsuguni, yayin da wasu hudun ke karbar magani saboda firgici, kamar yadda kafar yada labarai ta ruwaito.

Daga baya kungiyar Houthi ta tabbatar da cewa ta kai harin, tana mai cewa ta yi niyyar kai harin kan ma'aikatar tsaron Isra'ila da makami mai linzami mai karfin gaske.

Ƙarin labarai ????

1223 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin mutum 61 a Gaza yayin da adadin wadanda suka mutu ya haura 46,600

Akalla karin Falasdinawa 61 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza, wanda ya kara adadin wadanda suka mutu tun daga watan Oktoban 2023 zuwa 46,645, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ƙara da cewa wasu 110,012 kuma sun jikkata a harin da ake ci gaba da kai wa.

Ma'aikatar ta ce: Sojojin Isra'ila sun kashe mutum 61 tare da raunata wasu 281 a kisan gilla da aka yi wa iyalai hudu cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

0824 GMT — Yayin da ake ci gaba da samun ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta a Zirin Gaza, Isra'ila na ci gaba da yakin kisan kare dangi a Gaza inda ta kashe akalla wasu Falasdinawa 23 a yankunan Gaza a harin da ta kai ta sama cikin dare.

Wata majiyar lafiya a asibitin shahidai na Al-Aqsa da ke Deir al Balah a tsakiyar Gaza ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa, Falasdinawa 9 ne suka mutu da suka hada da mata da kananan yara a harin da Isra'ila ta kai kan wani gida da wani tanti da kuma wani wurin shan magani da ya zama mafaka ga 'yan gudun hijira. birnin.

Daya daga cikin matan na da juna biyu kuma jaririn bai tsira ba, kamar yadda asibitin shahidan Al-Aqsa, wanda ya karbi gawarwakin ya bayyana.

A kudancin Gaza, an kashe karin Falasdinawa 12 da suka hada da mata da yara a wasu hare-hare biyu da Isra'ila ta kai kan wasu gidaje biyu a garuruwan Khan Younis da Rafah, a cewar wata majiyar lafiya.

A birnin Gaza da ke arewacin yankin Falasdinawa, wata mata ta mutu, wasu kuma suka jikkata sakamakon wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wani gida da ke unguwar Al-Daraj, a cewar wata sanarwa da jami'an tsaron farar hula suka fitar.

Kamfanin dillancin labarai na Safa ya ce daya daga cikin 'yan jaridan ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a wani harin da Isra'ila ta kai a baya a Gaza ranar Litinin.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#