Sport
Dollar
35,4658
-0.04 %Euro
36,6765
0.23 %Gram Gold
3.066,9700
0.44 %Quarter Gold
5.028,7800
0.82 %Silver
34,7000
1.70 %Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi a Gaza — wanda a yau ya shiga kwana na 467 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 46,645 tare da jikkata mutum 110,012. A Lebanon, Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 4,063 tun watan Oktoban 2023.
Laraba, 15 ga watan Janairu, 2025
0750 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 40 a ƙasa da awa 24 a hare-haren da ta kai sassa daban-daban na Gaza a yayin da take ci gaba da kisan ƙare-dangi duk da yunƙurin tsagaita wuta da ake yi.
Kamfanin dillanacin labarai na Falasɗinu, WAFA, ya ambato wasu majiyoyi suna cewa Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 13 tare da jikkata gommai a wani hari ta sama da ta kai gidansu a kudancin birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza.
Kazalika wani hari da Isra'ila ta kai ta sama ya kashe Falasɗinawa bakwai a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat, kana wani harin ta sama ya kashe wani Bafalasɗine a wani yanki na sansanin da ke tsakiyar Gaza.
Bugu da ƙari, Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa a hare-hare ta sama guda biyu da ta kai gidajensu a sansanin 'yan gudun hijira na Bureij.
Ƙarin labarai ????
0737 GMT — Rundunar sojin Amurka ta fitar da bidiyon harin da ta kai wa mayaƙan Houthi
Cibiyar Bayar da Umarni ta rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta fitar da bidiyo na harin da ta kai a ƙarshen shekarar da ta wuce a wuraren da ta bayyana a matsayin maɓiyar mayaƙan Houthi a Yemen.
"Ranar 30 da 31 ga watan Disamba, Cibiyar Bayar da Umarni ta rundunar sojin Amurka ta kai hare-hare a maɓoyar mayaƙan Houthi da Iran take goyon baya," kamar yadda CENTCOM ta bayyana a saƙon da ta wallafa a shafin X, tare da bidiyon.
Ta ƙara da cewa ta kai hari a "cobiyoyin bayar da umarni da tabbatar da tsaro da kuma wuraren samar da makamai da ma'ajiyunsu" na ƙungiyar.
Comments
No comments Yet
Comment