Dollar

35,2438

0.22 %

Euro

36,7284

0.07 %

Gram Gold

2.982,0500

0.14 %

Quarter Gold

4.905,4200

0.00 %

Silver

33,8400

0.39 %

Continents

Categories

Kamfanin ya fada a wata sanarwa cewa an soke zirga-zirgar jiragensa daga Johannesburg zuwa Maputo da kuma na Istanbul zuwa Maputo.

Kamfanin jiragen sama na Turkiyya ya soke zirga-zirga zuwa Mozambique saboda rikici

Kamfanin jiragen sama na Turkiyya, Turkish Airlines ya soke zirga-zirgar jiragensa zuwa Maputo, babban birnin ƙasar Mozambique a ranar Alhamis.

Kamfanin ya fada a wata sanarwa cewa an soke zirga-zirgar jiragensa daga Johannesburg zuwa Maputo da kuma na Istanbul zuwa Maputo.

Matakin na zuwa ne sakamakon rikicin da ake fama da shi a ƙasar bayan da babbar kotun ƙasar ta tabbatar a ranar Litinin da cewa jam'iyya mai mulki ta Frelimo wadda ke kan mulkin tun shekarar 1975, ita ce ta lashe zaɓukan ƙasar na watan Oktoba.

An ayyana ɗan takarar jam'iyyar Frelimo, Daniel Chapo a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kashi 65 cikin 100 na ƙuri'un, sakamakon da ƙungiyoyin hamayya suka yi watsi da shi tare da zargin an yi maguɗi a zaɓen.

Ƙaruwar manyan laifuka

Tashin hankalin ya kuma jawo take dokokin tsaro sosai, da suka haɗa da fasa gidan yari inda fursunoni fiye da 1,500 suka tsere a lokacin boren a ranar Laraba.

Rikicin da ya ɓalle a cikin gidan yarin ya yi sanadin mutuwar mutum 33 sannan 15 suka jikkata.

Mace-macen na baya bayan nan sun sa yawan waɗanda suka mutu tun daga ranar 21 ga watan Oktoba a ƙasar ya kai 151, a cewar wata ƙungiya mai sa ido kan zaɓen, Plataforma Decide.

Ana hasashen za a samu ƙaruwar aikata laifuka a babban birnin ƙasar Maputi nan da awa 48, kamar yadda shugaban 'yan sandan ƙasar Bernardino Rafael ya sanar.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet