Dollar
35,2849
0.34 %Euro
36,7735
0.22 %Gram Gold
2.988,9400
0.37 %Quarter Gold
4.905,4200
0.00 %Silver
33,8400
0.38 %Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da zarge-zargen da shugaban mulkin soja na Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya yi a kan cewa Nijeriya da Faransa suna ƙoƙarin tayar da hargitsi a ƙasarsa.
Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da zarge-zargen da shugaban mulkin soja na Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya yi a kan cewa Nijeriya da Faransa suna ƙoƙarin tayar da hargitsi a ƙasarsa.
A wata sanarwa da Ministan Watsa Labaran Nijeriya, Mohammed Idris ya fitar ranar Alhamis, gwamnatin tarayyar ƙasar ta ce “Wadannan ikirari dai sun wanzu ne kawai a tunani, domin Nijeriya ba ta taba kulla wata alaka a bayyane ko a boye da Faransa ba - ko wata kasa - domin daukar nauyin hare-haren ta'addanci ko ta da hargitsi Jamhuriyar Nijar sakamakon sauyin mulki da aka samu a shugabancin kasar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa Shugaba Tinubu a matsayinsa na shugaban ƙungiyar ECOWAS, ya nuna jagoranci na gari, “tare da bude kofofin kananan ƙungiyoyin yanki domin sake shigar jamhuriyar Nijar cikin al’amura duk da halin da kasar ke ciki a siyasance.
“Nijeriya na ci gaba da jajircewa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma alakar diflomasiya mai dimbin tarihi da Nijar,” in ji sanarwar gwamnatin.
Tun da fari Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ne ya fada a wata hira da kafar yada labaran kasarsa cewa sun jima da bai wa gwamnatin Nijeriya bayanan sirri game da yadda Faransa take shirin kafa sansanin 'yan ta'adda na ƙungiyar Lakurawa a arewacin Nijeriya.
Janar Tiani ya yi zargin cewa gwamnatin Nijeriya na da masaniya game da ayyukan Lakurawa da kuma yin watsi da shawarwarin da suka ba ta game da ‘yan ta’addan.
Minista Mohammed Idris ya ƙara da cewa Rundunar Sojin Nijeriya tare da hadin guiwar takwarorinta na rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa, na samun nasarar dakile ayyukan ta’addanci a yankin.
“Don haka, shirme ne a ce Nijeriya za ta hada baki da duk wani karfi na kasashen waje domin kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron wata kasa makwabciyarta.”
Tun bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a shekarar 2023 alaƙa tsakanin ƙasashen biyun maƙwabtan juna ke ta yin tsami, lamarin da har ya kai ga Nijar barazanar ficewa daga ƙungiyar ECOWAS, wadda Tinubu na Nijeriya ke jagoranta.
“Nijeriya ba ta goyon bayan ta’addanci” Gwamnatin Nijeriya ta ce ita ko jami’anta ba su taba sa hannu wajen ba wa wata kungiyar ta’addanci makamai ko tallafa wa wata kungiyar ta’addanci ta kai hari a Jamhuriyar Nijar ba.
Bugu da kari kuma ta nanata cewa, babu wani yanki na Nijeriya da aka mika wa wata kasa ta ketare don ayyukan zagon kasa ga Jamhuriyar Nijar.
“Muna kara jaddada cikakken goyon bayanmu ga manyan jami'an gwamnatin Nijeriya bisa jajircewar da suke yi na samar da zaman lafiya da tsaro tsakanin gwamnati da al'ummar Nijeriya da Nijar, da kuma kokarin da suke na samar da hadin gwiwa mai karfi a yankin ECOWAS.”
A cikin hirar ta Janar Tiani, ya yi ta jaddada zargin Nijeriya da yin alaƙa da Faransa don tayar da tashin hankali a Nijar.” “Hakika Nijeriya tana da al’adar da ta dade tana kare ‘yancinta da kuma yankinta.
Ba kamar wasu kasashe ba, Nijeriya ba ta taba barin wasu kasashen waje su kafa sansanonin soji a kasarta ba. “Wannan yana nuna sadaukarwarmu ga 'yancin kai na ƙasa da jagorancin yanki.
Comment