Dollar
35,1874
-0.11 %Euro
36,7611
0.05 %Gram Gold
2.968,2700
0.17 %Quarter Gold
4.905,4200
-0.07 %Silver
33,7200
0.42 %Wani bincike na baya bayan nan ya ce yawan gurbataccen hayakin carbon da shafin TikTok ke fitarwa a yanzu zai iya wuce yawan gurbataccen hayakin da ƙasa kamar Girka za ta fitar na shekara ɗaya.
Akwai yiwuwar ba za ka kai ƙarshen maƙalar nan ba za ka koma ka ci gaba da shawagi a shafin Instagram ko TikTok ko duk wani shafi da ka fi so na sada zumunta.
Wannan ɗabi’a ta jawo wani irin tsanani ga mahalli da ba a hango shi, yayin da lamarin ke jawo mummunan tasiri – wanda mai yiwuwa mun sani ko ba mu sani ba.
Wani bincike na baya bayan nan da Greenly, wani kamfani mai kula da sinadarin carbon da ke birnin Paris ya yi, ya ce yawan gurbataccen hayakin carbon da shafin TikTok ke fitarwa a yanzu zai iya wuce yawan gurbataccen hayakin da ƙasa kamar Girka za ta fitar na shekara ɗaya, lamarin da ya sa aka sake yin nazari kan tasirin dandalin kan rikicin sauyin yanayi.
Tiktok wanda aka ƙaddamar da shi a 2016 ya yi matuƙar farin jini da samun karbuwa a ƙsa da shekara 10, musamman a tsakanin matasa ‘yan Gen Z, kuma a yanzu fiye da mutum biliyan ɗaya ne suke amfani da shi a duniya.
Sai dai, wannan karbuwa tasa ta zo da matsaloli birjik.
Binciken Greenly ya nuna cewa duk mai amfani da shafin Tiktok yawanci yakan samar da gurbatacciyar iskar carbon ta CO2e adadin kilogiram 48.49 duk shekara, mafi yawa da aka fi fitarwa a tsakanin dukkan shafukan sada zumunta.
YouTube ke biye da shi inda duk mai amfani da shafin kan samar da kilogiram 40.17 na gurbatacciyar iska, yayin da mai amfani da Instagram kuma kan samar da kilogiram 32.52.
Don a fahimci abin sosai, Hukumar Kare Muhalli ta ce wannan gurɓatacciyar iska daidai take da a tuƙa mota mai amfani da fetur tsawon tafiyar mil 123 (TikTok), da mil 102 ga (YouTube), da kuma mil 82.8 (Instagram).
To amma yaya gaskiyar waɗannan binciken, kuma me suke nufi?
Faffaɗan batun
Abubuwan da suka shafi gurbatacciyar iskar carbon yawanci ana bayyana su daidai da iskar carbon dioxide (CO2e), wanda ke wakiltar tasirin nau’ukan iskar gas da haduwa da zafi suna yawo a sararin samaniya wato greenhouse gases.
Da yake magana da TRT World, Mataimakin Farfesa Ahmet Aygun, ya bayyana cewa ingantattun ƙididdiga sun dogara ne a kan bayanan farko da na biyu.
"Bayani na farko daga takamaiman ma'auni, tare da bayanai na biyu daga wallafe-wallafen kimiyya da nazarin ƙididdiga, na da mahimmanci," in ji Aygun, wanda ya ƙware kan sarrafa gurɓatacciyar iska daga masana'antu kuma ya mallaki kamfanin magance matsalar muhalli na GNA R & D.
"Yana da muhimmanci a gano tare da ƙididdige duk hayaƙin da ake samarwa kai tsaye da ma wanda ba kai tsaye ba, a yi la’alari da kuma sanya mafiya muhimmancin ta hanyar amfani da hanyoyin bincike da suka fi dacewa."
Sai dai, saboda rashin hanyoyin samun bayanai daga ByteDance, wanda shi ne mamallakin kamfanin Tiktok, binciken Greenly ya yi amfani da bayanan mataki na biyu ne, wanda ke ƙara rashin tabbas.
Aygun ya jaddada cewa bayanan fitar da gurbataccen hayaƙi na TikTok na daga cikin wanda babu gaskiya sosai a ciki a masana'antar, wanda yake bukatar yin taka tsantsan wajen fayyace shi.
Ba kamar kamfanoni irin su Meta da Google ba, waɗanda ke fitar da cikakkun rahotanni masu ɗorewa, TikTok yana ba da taƙaitaccen bayani game da yanayin gurbataccen hayaƙin sa da ƙoƙarin muhalli.
Duk da haka, Aygun ya yarda cewa rahoton ya ba mu faffadan bayani mai zurfi game da yadda kafofin sada zumunta ke yin mummunan tasiri a kan yanayi kuma ya kamata masuruwa da tsaki a gwamnatoci su dauki abin da mahimmanci.
Amma ta yaya kafofin sada zumunta ke haifar da gurɓataccen hayaƙin carbon?
Tsarin iskar CO2
Ana tafiyar da shafukan sada zumunta ne ta wani tsari mai buƙatar makamashi mai ƙarfi.
Rumbun bayanai, waɗanda suke adana da sarrafa bayanai masu matuƙar yawa, na buƙatar lantarki don tafiyar da na’urorinsu da kuma sanyaya su.
Na'urori kamar wayoyin hannu da kwamfutar hannu, da kwamfutocin tafi-da-gidanka suna ƙara ba da gudunmawa wajen yawan amfani da makamashi.
Bugu da ƙari, sarrafa bayanai ta hanyoyin sadarwa na duniya, da suka hada da Wi-Fi da tsarin salula, yana ƙara samuwar gurbatacciyar iskar carbon.
Kamar yadda Aygun ya bayyana, "Kafofin sada zumunta wani tsari ne na cibiyar sadarwa ta intanet, kuma yanayinsu na dijital yana haifar da karuwar bukatar makamashi, wanda a yanzu yake ƙara haifar da gurbatacciyar iskar carbon."
Lantarki, wanda har yanzu ana samunsa daga burbushin fetur, ya sa amfani da kafofin sada zumunta yana ba da gudunmowa sosai ga samar da hayaƙin CO2.
Duk shawagi da mutum zai yi na minti ɗaya a TikTok yana samar da giram 2.921 na gurɓatacciyar iskar CO2e, inda yake ƙasa kaɗan da wadda ake samarwa a Youtube mai giram 2.923 da Instagram mai giram 2.912.
Akwai ɗan bambanci kaɗan tsakanin Youtube da Tiktok. Don haka mene ne ya sa gurbatacciyar iskar da ake fitarwa a TikTok ta zama daban idan aka kwatanta da sauran shafukan, a cewar Greenly?
Alƙaluma na jaraba
Tsarin TikTok, wanda aka yi shi “Musamman don Ku” wato "For You Page," yana taka muhimmiyar rawa wajen ƙara samar da gur batacciyar iska.
Wannan fasalin yana sa masu bibiya su yi ta kallon gajerun bidiyoyi da suka fi jan hankalinsu da aka tsara musamman yadda za su ci karo da su, ta yadda aƙalla a rana za su yi shawagi na tsawon minti 45.5 — abin da ya sa ya zarta na Instagram mai minti 30.6, a cewar jaridar Guardian.
Instagram kadai na nuna ma'aunin hayakin da kafafen sada zumunta ke fitarwa.
A cikin 2020, Rabih Bashroush, farfesa a Jami'ar Gabashin London, ya kiyasta cewa a duk lokacin da Cristiano Ronaldo ya saka hoto a Instagram, makamashin da mabiyansa miliyan 190 ke buƙata don ganin hoton - a lokacin - na iya bai wa gida daya lantarki na tsawon shekara biyar zuwa shida.
Duk da cewa yawan masu amfani da Instagram ya nunka na TikTok sau 1.5, jimlar lokacin da ake shafewa a TikTok ya fi yawa da kashi 20 cikin ɗari.
A cewar kamfanin data.ai, yawanci masu amfani da TikTok kan shafe aƙalla awanni 34 da mintuna 15 a kowane wata a kan shafin, fiye da awanni 16 da mintuna 49 da akan yi a Instagram.
Wannan tsawaita shawagi yana haifar da ƙaruwar fitar da gurɓatacceiyar sikar carbon.
Alexis Normand, Shugaban kamfanin Greenly, ya lura cewa dabi'ar jarabtuwa da shiga TikTok tana haifar da yawaitar fitar da gurɓatacciyar iskar carbon.
Babban batun
Kamar yadda Aygun ya nuna, matsalolin muhalli da TikTok ke jawowa suna nuna babban batun a cikin masana'antar fasaha.
Kafofin sada zumunta a jumlace suna samar da kusan tan miliyan 262 na gurbatacciyar iskar CO2e a kowace shekara - daidai da jimillar hayakin da Malaysia ke fitarwa.
Yayin da yawancin manyan kamfanonin fasaha suke yin alkawarin komawa amfani da makashin da ake sabuntawa, rahoton ya bayyana irin yadda ba a ba da rahotanni sosai a kan gurɓataccen hayaƙi— da ƙaruwar kashi 662 fiye da yadda ake bayyanawa.
Daga shekarar 2020 zuwa 2022, ainihin hayakin da Google da Microsoft da Meta, da cibiyoyin bayanan cikin gida na Apple suke fitarwa sun fi fiye da yadda aka rawaito.
Cibiyoyin bayanai sun riga sun cinye kashi 1 zuwa 1.5 na wutar lantarki na duniya, adadi da ake tsammanin zai yi ƙru saboda haɓakar Ƙirƙirarriyar Basira, AI.
Bugu da ƙari, aikace-aikacen AI kamar ChatGPT suna buƙatar makamashi kusan sau 10 fiye da na sauran ayyuka, inda ake hasashen gurbataccen hayaƙin da ake fitarwa a duniya zai kai ton biliyan 2.5 na CO2e nan da 2030.
Comment