Sport
Dollar
38,4292
0.2 %Euro
43,8350
-0.02 %Gram Gold
4.095,0600
-0.84 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ranar Asabar 26 ga Afrilu za a buga wasan ƙarshe na cin kofin Copa Del Rey na Sifaniya tsakanin Barcelona da Real Madrid.
Yayin da ake dakon buga wasan ƙarshe na cin kofin Copa Del Rey na Sifaniya tsakanin Barcelona da Real Madrid ranar Asabar, taƙaddama ta kaure kan wanda zai yi alƙalancin wasan.
Ana sa ran wasan wanda zai fayyace ƙungiyar da za ta ɗaga kofin na Sifaniya zai yi zafi matuƙa, kasancewar ƙungiyoyin biyu da magoya bayansu sanannu ne kan daɗaɗɗiyar hamayya a tarihi.
Rahotannin da ke fitowa ranar Juma’a, kwana guda kafin wasan, suna cewa Real Madrid tana fatan za a sauya alƙalin da aka shirya zai raba gardama a wasan na maraicen Asabar.
Martanin Real Madrid
An nuno alƙalin wasan Ricardo de Burgos Bengoetxea yana ɓarkewa da kuka a yayin taron manema labarai na shirye-shiryen wasan.
Bengoetxea ya yi hawayen ne saboda ya ce an saki wani bidiyo a shafin Real Madrid TV, wanda ke nuna shakku kan ko zai yi adalci a aikinsa na alƙalancin.
Bayan jawabin alƙalin wasa, an ambato Real Madrid na cewa sun ji “mamaki” da jin kalaman alƙalin wasan, wanda ke nuna yana da damuwa kan ƙungiyar.
Madrid ta yi imanin cewa alƙalin “bai shirya yin alƙalancin wasan ba bayan da fashe da kuka” awanni 24 kafin take wasan da za a yi a birnin Seville.
Sai dai kuma, ana hasashen cewa Real Madrid ba za ta samu yadda take so ba gabanin wasan, saboda zai yi wuya a iya sauya alƙalin wasan a daidai wannan mataki.
Comments
No comments Yet
Comment