Dollar

35,1979

0.07 %

Euro

36,6586

0.02 %

Gram Gold

2.967,9400

0.30 %

Quarter Gold

4.910,7200

0.00 %

Silver

33,6200

0.11 %

Continents

Categories

Mutanen da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta gurfanar a kotu bisa zargin aikata laifukan ta’addanci tare da ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji sun musanta tuhume-tuhume 11 da aka  yi musu.

Kotu ta umarci a ci gaba da tsare mutanen da ake zargi da alaƙa da Bello Turji

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja Babban Birnin Nijeriya ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wasu ‘yan ta’adda uku daga cikin mutum takwas da ake zarginsu da alaka da ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji a gidan yarin Kuje.

A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da mutanen a gaban kotun bisa zargin aikata laifukan ta’addanci, ko da yake sun musanta tuhume-tuhume 11 da ake zarginsu da aikatawa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare Musa Muhammad Kamarawa da Abubakar Hashimu wanda aka fi sani da Dakta da Samuel Chinedu, har zuwa ranar 10 ga watan Fabrairun 2025 inda za ci gaba zaman shari'ar.

Duk da cewa sunayen mutum takwas aka gabatar a kotun, mutum uku ne suka hallara sauran kuma ana neman su ruwa-a-jallo.

Tun da farko dai sunayen mutum huɗu lauyan gwamnati, David Kaswe, ya gabatar a matsayin waɗanda za su hallara a gaban kotun - ciki har da Lucky Chukwuma - amma sai mutum uku kaɗai suka gabatar da kansu ga mai shari'ar.

Laifukan da ake zargin da aikatawa

Ana zargin waɗanda ake tuhuma ne da samar da haramtattun kayayyaki aiki ga ƙungiyoyin ta'addanci ƙarƙashin jagorancin Bello Turji da Kachalla Halilu da Danbokolo, da Lawali, da Atarwatse, da Buderi da dai sauransu, daga ciki har da miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi da kayan abinci, kayan soji da na 'yan sanda da makamai.

Kazalika ana zarginsu da samar da takalma da huluna da kayayyakin gini da buhunhunan siminti da ƙusoshi da sanduna da sauran kayayyaki ga sansanonin ‘yan ta’adda da ke dazuzzukan jihohin Zamfara, da Sokoto, da kuma Kaduna.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet