Dollar

35,4810

-0.02 %

Euro

36,5318

0.66 %

Gram Gold

3.048,7000

0.36 %

Quarter Gold

4.987,7800

-0.12 %

Silver

34,2000

1.20 %

Continents

Categories

Gwamnatin Mali ta ƙwace zinaren ne da darajarsa ta kai dala miliyan 180 daga kamfanin na Canada, a yayin da ake ci gaba da taƙaddama ta shari’a kan bashin da Mali take bin kamfanin.

Mali ta ƙwace zinare tan uku daga kamfanin Barrick na Canada

Gwamnatin sojin Mali ta fara ƙwace zinaren da kamfanin haƙar ma’adanai na Kanada Barrick ya tara, a wani ɓangre na taƙaddamar shari’a kan rabon kuɗin da ake samu daga zinaren, wanda gwamnatin ƙasar take bin kamfanin, a cewar wata wasiƙa ta cikin gida da kamfanin na Barrick ya aike, wacce kamfanin dillancin labarai na AP ya gani.

Wasiƙar wacce shugaban kamfanin Mark Bristow ya aike wa ma’aikata ɗauke da kwanan watan ranar Litinin, ta ce kamfanin yana jiran “tabbaci a hukumance na karɓar zinaren daga bankin Malian Solidarity Bank,” wanda bankin gwamnatin ne.

Ƙwace zinaren ya biyo bayan takardar gargaɗi daga babban alƙalin Mali dake bincike kan batun Boubacar Moussa Diarra, wanda ya aike a wannan watan, yana cewa za a ƙwace tan uku na zinare.

A ranar Litinin, wani babban manajan Barrick ya tabbatar da cewa gwamnatin soji ta ƙwace tan uku, kuma an ajiye su a babban birnin ƙasar Bamako. Manajan ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana kan batun ba a bainar jama’a.

Sammacin kama shugaban kamfanin

A cewar babban manajan, an ɗauki zinaren ne a wani wajen haƙar zinare kusa da Kayes a yammacin ƙasar, kuma an tafi da shi zuwa babban birnin kasar ranar Asabar a manyan motoci da kuma jirgin sama.

Har kawo yanzu hukumomin Mali ba su mayar da martani ba kan batun.

Ƙwace zinaren wanda darajarsa ta kai kimanin dala miliyan 180, na daga wani ɓangare na taƙaddamar da ake yi kan kuɗaden da gwamnati ke bin kamfanin.

A watan Disamba, Mali ta ba da sammacin kama Bristow saboda zargin fitar da kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, ta kuma bayar da umarnin ƙwace ma’adanar zinaren Brrick. Kamfanin ya yi tayin biyan dala miliyan 370.

A baya, gwamnatin Mali ta kama wasu manyan jami’an kamfanin na haƙar ma’adanai na Kanada huɗu, a wani ɓangare na taƙaddamar.

Sai dai an sake su nan da nan.

Mali na daga ƙasashen Afirka da ke kan gaba wajen samar da zinare, amma ta shafe shekaru da dama tana fama da yaƙe-yaƙen ‘yan tawaye, da mummunan talauci da matsananciyar yunwa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#