Dollar

35,5149

0.08 %

Euro

36,6156

0.04 %

Gram Gold

3.052,4900

-0.03 %

Quarter Gold

4.987,7800

0.00 %

Silver

34,0300

-0.25 %

Continents

Categories

Masu aikin sa kai sun ce an kashe mutane da dama a ruwan bama-baman da aka yi kan mai-uwa-da-wabi a yammacin Omdurman yayin da yaƙi ke ta'azzara tsakanin rundunar soji da ta sa kai ta RSF.

Yaƙin Sudan: Aƙalla mutum 120 aka kashe a kusa da Khartoum

Masu aikin agaji na sa kai a Sudan sun ce ruwan bama-baman da aka yi a Greater Khartoum ya jawo asarar rayukan aƙalla mutum 120, a yayin da faɗa tsakanin sojojin ƙasar da rundunar sa kai ke ta'zzara.

"Ruwan bama-baman na kan mai-uwa-da-wabi" da aka yi a ranar Litinin a yammacin Omdurman, birni na biyu mafi girma a ƙasar da ke kusa da Nile River, sun jawo asarar rayukan fararen hula 120, a ceewar Cibiyar Taimakon Gaggawa ta Ombada, wani sashe na masu aikin agaji na sa kai da ke aiki a faɗin ƙasar.

Sashen ya ce yawan waɗanda suka mutun tun waɗanda aka tattara ne da farko, sannan kuma bai faɗi ko wane ɓangare ne ya kai harin ba.

Masu aikin ceton sun ce ana tsananin fama da ƙarancin kayayyakin amfanin asibiti a yayin da ma'aikatan lafiya ke fafutukar duba "mutane da dama da suka jikkata" sakamakon ɓarin wutar.

Hare-hare daga tsallaken kogi

Tun watan Afrilun 2023 Sudan ke cikin yaƙi tsakanin dakarun gwamnati da na rundunar sa-kai kan batun neman iko da ƙasar.

Mafi yawan yankin Omdurman na ƙarƙashin ikon rundunar sojin ƙasar, yayin da rundunar sa-kai ta RSF ke riƙe da arewacin Khartoum da ma wasu sassan babban birnin ƙasar.

Mazauna yankin Greater Khartoum daga dukkan ɓangarorin Nile suna yawan ba da rahoton cewa ana musu ruwan wuta da ke faɗawa kan gidajensu suna shafar fararen hula.

A ranar Lahadi, masu aikin ceto a yankin Ombada na Omdurman sun ba da rahoton cewa ana fama da matsanancin yanayi a fannin lafiya, inda fiye da mutum 70 suka mutu daga tsakanin watan Agusta zuwa Disamba, lamarin da aka alaƙanta da matsananciyar tamowa da yunwa da amaleriya da kuma gudawa.

Faɗawa yunwa

Ruwan wutar da aka yi na ranar Litinin ya faru ne a yayin da faɗan da ake gwabzawa tsakanin rundunar soji da ta RSF ya ta'azzara a makonnin baya bayan nan, inda aka shafe fiye da wata 20 ana yaƙi.

Yankin tashar jiragen ruwa ta Port Sudan, inda nan ne mazaunin rundunar soji da ke ɓarin gwamnati ke zaune, sun rasa lantarki a ranar Litinin bayan da wani harin jirgi marar matuƙi da ake zargin rundunar RSF ta kai ya shafi madatsar ruwan da ke bai wa arewacin ƙasar wuta.

Harin na zuwa ne bayan da rundunar soji ta ƙwace Wad Madani, babban birnin jihar tsakiya ta Al-Jazira, bayan shafe fiye da shekara ɗaya rundunar RSF na iko da shi.

Baya ga rusa abubuwan more rayuwa da yaƙin ya yi a Sudan, ya kuma jawo asarar rayukan dubban mutane, da raba mutum miliyan 12 da muhallansu da kuma jefa ƙasar a cikin yunwa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#