Sport
Dollar
35,4893
0.05 %Euro
36,6448
0.20 %Gram Gold
3.076,8600
0.08 %Quarter Gold
5.028,7800
0.00 %Silver
34,9900
-0.14 %Kashin farko na tsagaita wutar na tsawon mako shida zai fara ne daga ranar Lahadi, 19 ga Janairu, da ya haɗa da fara janye sojojin Isra’ila sunnu a hankali daga tsakiyar Gaza.
Ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da Isra'ila sun cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo ƙarshen yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, in ji Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, mai shiga tsakani na Qatar.
Ana iya gano cikakkun bayanai game da yarjejeniyar daga kalaman mai shiga tsakani Qatar da Shugaban Amurka Joe Biden suka yi.
Tsagaita wutar za ta ƙunshi matakai uku kuma masu shiga tsakani na Amurka da Qatar da Masar ne za su sanya ido a kai.
Kashi na farko
Kashi na farko na tsagaita wutar na makonni shida da zai fara daga ranar Lahadi 19 ga watan Janairu ya haɗa da janyewar sojojin Isra'ila sannu a hankali daga tsakiyar Gaza da kuma komawar Falasɗinawa da suka yi gudun hijira zuwa arewacin Gaza.
Isra'ila za ta janye sojojinta daga cibiyoyin al'ummar Gaza zuwa yankunan da ba su wuce mita 700 daga kan iyakar Gaza da Isra'ila ba.
Yarjejeniyar dai ta buƙaci a ba da damar shigar da manyan motoci 600 na kayan agaji zuwa Gaza a kowace rana da aka tsagaita wutar, 50 daga cikinsu ɗauke da mai, tare da tura 300 daga manyan motocin zuwa arewacin yankin.
Hamas za ta saki fursunonin Isra'ila 33 da ta yi garkuwa da su, da suka haɗa da mata (sojoji da farar hula), da waɗanda ba sojoji ba ne 'yan ƙasa da shekara 19, da kuma maza da suka haura shekara 50. Hamas za ta saki waɗanda aka yi garkuwa da su mata 'yan ƙasa da shekaru 19 da farko, sai kuma maza da suka haura shekara 50.
Isra'ila za ta saki fursunonin Falasdinawa da ba a bayyana adadinsu ba a madadin duk wani farar hula da aka yi garkuwa da shi.
Har ila yau Isra'ila za ta bar Falasɗinawa da suka samu raunuka su bar Gaza domin neman magani, tare da buɗe mashigar Rafah da iyakar Masar kwanaki bakwai bayan fara aiwatar da matakin farko.
Kashi na biyu
Za a fara tattaunawa kan kashi na biyu na yarjejeniyar ne a rana ta 16 daga mataki na farko, kuma ana sa ran za a haɗa da sako dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su da suka ƙunshi sojojin Isra'ila maza, da tsagaita wuta ta din-din-din da kuma janye sojojin Isra'ila gaba ɗaya.
Kashi na ƙarshe
Ana sa ran kashi na uku zai haɗa da dawo da dukkan gawawwakin da suka rage da kuma fara aikin sake gina Gaza, wanda kasashen Masar da Qatar da Majalisar Ɗinkin Duniya za su kula da shi.
Comments
No comments Yet
Comment