Sport
Dollar
35,4657
-0.05 %Euro
36,5385
-0.16 %Gram Gold
3.068,6100
0.50 %Quarter Gold
5.028,7800
0.82 %Silver
34,8900
2.28 %An bayyana dalilan da suka sanya aka jinkirta fara gasar ƙasashen Afirka ta 'yan wasan cikin gida da ake kira CHAN, wadda za a yi a Kenya, Tanzania da Uganda, zuwa watanni shida.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka, CAF ta sanar da jinkirta fara gasar ƙasashen Afirka ta 'yan wasan cikin gida da ake kira CHAN, wadda za a yi a ƙasashen Kenya da Tanzania da Uganda.
Ranar Talata ne CAF ta dakatar da gasar da ta rage makonni kaɗan kafin farawa wadda za ta ƙunshi tawagar ƙasashe 19, wadda aka shirya fara ta ranar 1 ga Fabrairu, inda yanzu za a buga ta a Agusta mai zuwa.
Duk da cewa hukumar CAF ta ce jinkirin ya zama dole ne saboda ƙasashe uku masu masaukin baƙi ba su kammala shirya wuraren wasannin ba, a yanzu an fara gano cewa akwai wasu dalilan daban.
Ƙasashen uku da ke gabashin Afirka su ne aka shirya za su karɓi baƙuncin babbar gasar AFCON ta 2027, kuma an shirya cewa gasar CHAN ta bana za ta zama zakaran gwajin dafi kan shirinsu na gudanar da gasanni.
Sanarwar CAF ta ce, "An samu babban cigaba a shirin da Kenya, Tanzania da Uganda ke yi na gina filayen wasa, da wuraren atisaye, da otal-otal, da asibitoci da sauran kayayyakin da ake buƙata don nasarar gasar CHAN".
1) Jinkirin shirye-shirye
Ƙwararru daga hukumar CAF ne suka ba da shawarar cewa ana buƙatar ƙarin lokaci don tabbatar da an kammala shirya kayayyaki da wuraren da ake buƙata don gudanar da gasar cikin nasara.
A makonnin da suka gabata, shugaban hukumar CAF Patrice Motsepe ya je Kenya don ganawa da shugaban ƙasar William Ruto, don ganin an ƙara saurin shirye-shiryen fara gasar.
Zuwa yanzu, CAF ta ce jingine fara gasar zuwa Agusta ya zama dole saboda tabbatar da kammala shirye-shirye.
2) Ƙauracewar wasu ƙasashe
An ƙaddamar da gasar CHAN a karon farko a 2007, don bai wa 'yan wasan da ke taka leda cikin Afirka dama, bayan ganin yawa da fifikon 'yan wasan da ke buga ƙwallo a ƙasashen wajen nahiyar.
Sai dai duk da an gudanar da gasar karo bakwai duk bayan shekaru biyu, gasar ta gaza samun karɓuwa, wanda ya janyo hukumar CAF ta fara tunanin soke ta daga jadawalin gasanninta.
A bana, wasu manyan ƙasashen Afrika a harkar ƙwallo kamar Algeria, Masar, Afirka ta Kudu, da Tunisia sun ƙauracewa shiga neman cancantar buga gasar ta bana, wadda aka kammala a watan jiya.
3) Gasannin ɗaiɗaikun ƙasashe
Wasu masana ƙwallo na ganin CAF tana ƙoƙarin ganin ƙasashen da ke ciki gasar sun kammala gasarsu ta cikin gida zuwa Agusta, saboda 'yan wasan cikin gidan ne za su buga gasar ta CHAN.
Idan da gasar ta guda a watan Fabrairun nan kamar yadda aka shirya asali, to za ta haifar da tsaiko ko tasgaro ga ƙungiyoyin da suka bayar da 'yan wasansu, inda za su rasa zaratan 'yan wasa, wanda zai iya shafar tagomashin ƙungiyoyin.
Baya ga cewa 'yan wasan za su gaza bugawa ƙungiyoyinsu na cikin gida, akwai yiwuwar za su samu gajiyar da za ta shafi kuzarinsu bayan komawa ƙasashensu.
Gasar CHAN za ta gudana ne a ƙasashe uku, inda 'yan wasa za su yi ta tafiye-tafiye tsakanin ƙasashen.
A yau Laraba ne CAF za ta bayyana jadawalin yadda za a kara tsakanin ƙasashe a wani biki da zai gudana a birnin Nairobi na Kenya da maraice.
Comments
No comments Yet
Comment