Dollar

38,2552

0.34 %

Euro

43,8333

0.15 %

Gram Gold

4.076,2000

0.31 %

Quarter Gold

6.772,5700

0.78 %

Silver

39,9100

0.36 %

Ankara ta buƙaci ƙasashen duniya su tashi tsaye domin martani kan toshe hanyoyin shiga Gaza da Isra'ila ta yi.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan ya tattauna da wakilan Hamas kan tsagaita wuta a Gaza

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna da shugaban majalisar gudanarwar kungiyar Hamas Muhammad Darwish da wakilan ofishin siyasa na kungiyar a birnin Ankara inda suka tattauna kan rikicin Gaza da kuma kokarin cim ma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, a cewar majiyoyin diflomasiyya.

Taron wanda da aka yi a ranar Asabar, ya nuna damuwar da ke kara nuna cewa Isra’ila na amfani da toshe hanyoyin shiga Gaza don kashe al’ummar Falasdinu da gangan ta hanyar ɗakile ayyukan jin kai.

Fidan da jami’an Hamas sun yi kira ga ƙasashen duniya su ƙara matsa lamba don tabbatar da isar da abinci, magunguna, da muhimman kayayyaki zuwa Gaza ba tare da samun cikas ba.

Watsi da batun tilasta wa Falasɗinawa barin muhallansu

Duka ɓangarorin biyu sun yi kakkausar suka ga abin da suka bayyana a matsayin yunƙurin Isra'ila na tilasta wa Falasɗinawa ƙaura daga ƙasarsu ta haihuwa. An yi Allah wadai da irin waɗannan ayyuka a matsayin keta dokokin ƙasa da ƙasa da kuma wani mummunan tashin hankali da ke barazana ga zaman lafiya a yankin.

Taron ya kuma yi tsokaci kan halin da ake ciki a Gaɓar Yamma da Jordan da ta mamaye, inda Turkiyya ta yi gargaɗin cewa ayyukan da Isra'ila ke yi na tabbatar da mamaya sun kai wani mataki mai haɗari. Waɗannan matakan, in ji jami'ai, suna yin barazana kai tsaye ga zaman lafiyar yankin na dogon lokaci da ƙoƙarin samar da zaman lafiya.

Kira domin haɗin kan Falasɗinawa

Kokarin samar da sulhu tsakanin ɓangarorin Falasdinawa shi ma yana cikin ajandar.  Mista Fidan ya jaddada muhimmancin haɗin kan Falasɗinawa tare da jaddada cikakken goyon bayan Turkiyya ga duk wani shiri na cim ma wannan buri.

Tattaunawar shugaban hukumar leƙen asirin Turkiyya da tawagar Hamas

Tun da farko a wannan rana, Ibrahim Kalin, shugaban hukumar leƙen asiri ta Turkiyya (MIT), shi ma ya gana da tawagar Hamas ƙarƙashin jagorancin Muhammad Darwish, shugaban majalisar shura na ƙungiyar.

Babbar tattaunawar ta mayar da hankali ne kan daidaita ayyukan agajin jin kai da kuma ƙarfafa haɗin-gwiwar ƙasa da ƙasa don magance munanan yanayin da mazauna Gaza miliyan 2.3 ke fuskanta.

Mayar da hankali kan tallafin jin ƙai

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, ajandar farko ita ce tabbatar da isar da kayan agaji cikin sauri da inganci, musamman abinci, yayin da Falasɗinawa a Gaza ke ci gaba da fuskantar matsanancin ƙarancin abinci sakamakon ƙawanya da kuma ci gaba da kai hare-hare da sojojin Isra'ila suke yi.

Tattaunawar ta kuma bayyana shirye-shiryen Turkiyya na bayar da ƙarin gudunmawar kayayyaki da amfani da hanyoyin diflomasiyya don hanzarta kai agaji.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#