Sport
Dollar
38,2552
0.34 %Euro
43,8333
0.15 %Gram Gold
4.076,2000
0.31 %Quarter Gold
6.772,5700
0.78 %Silver
39,9100
0.36 %A sanarwar da NDLEA ɗin ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa an ɓoye ɗauri 20 na hodar wanda jumullar nauyinsu ya kai gram 500 a cikin littattafan addini.
Hukumar NDLEA a Nijeriya da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta yi nasarar kama hodar ibilis wadda aka boye a cikin littattafan addini da ake shirin kaiwa Saudiyya.
A sanarwar da NDLEA ɗin ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa an ɓoye ɗauri 20 na hodar wanda jumullar nauyinsu ya kai gram 500 a cikin littattafan addini.
Hukumar ta ce jami’an hukumar sun gano hodar ne a yayin da suke gudanar da bincike a wani kamfanin da ke jigilar kayayyaki a Legas a ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, yayin da yake shirin kai kayayyakin zuwa Saudiyya.
Baya ga haka hukumar ta NDLEA ta yi ƙarin bayani game da wasu jerin nasarori da ta samu a makon da ya gabata a ƙasar ta fannin daƙile fataucin miyagun ƙwayoyi.
A wani kamfanin na daban da ke jigilar kayayyaki, hukumar ta NDLEA ta ce ta kama kilo 2.8 na tabar wiwin Loud wadda aka shigar da ita ƙasar daga Amurka.
A Kano, jami’an NDLEA sun kama wani matashi ɗan shekara 22 da haihuwa da ke sayar wa ‘yan fashi da haramtattun kayayyaki a lokacin da suke sintiri a hanyar Bichi zuwa Kano, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Katsina ɗauke da kwalabe 277 na allurar pentazocine a ɗaure a cinyarsa da kuma cikin al’aurarsa. An kama shi ne a ranar Lahadi 13 ga watan Afrilu, yayin da aka kama wani da ake zargi mai suna Mohammed Abdulrahman Abdulaziz, mai shekaru 43, a ranar Lahadin da ta gabata a unguwar Rimin Kebe da ke Nasarawa, Kano tare da sunƙin wiwi nau’in skunk 68, wanda nauyinta ya kai kilo 30.
Comments
No comments Yet
Comment