Dollar

37,9423

-0.12 %

Euro

41,1567

-0.07 %

Gram Gold

3.787,4700

-0.63 %

Quarter Gold

6.210,1600

0 %

Silver

41,3700

-0.7 %

Yankin Tafkin Chadi yana fama da hare-haren ‘yan bindiga ciki har da ‘yan kungiyar ISWAP da Boko Haram, waɗanda suka ƙaddamar da yaƙi a arewa maso gabashin Nijeriya a shekarar 2009 kuma sun kashe dubban mutane.

Nijar ta fita daga rundunar tsaron haɗin gwiwa ta MNJTF

Nijar ta fita daga rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Tafkin Chadi da ke yammacin Afirka yayin da take ƙoƙarin inganta tsaro kan albarkatun mai a cikin gida, in ji gwamnatin ƙasar a sanarwar da ta bayar a gidan talbijin na ƙasar.

Rundunar tsaro ta haɗin gwiwa ta (MNJTF), wadda ke da sojoji daga Nijeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru, tana aiki domin daƙile ayyukan masu tayar da ƙayar baya tun shekarar 2015, amma rarrabuwar kai da matsalar rashin daidaito na hana ta samun nasara sosai, lamarin da ya sa ƙungiyoyin ‘yan bindiga a yankin cin karensu ba babbaka.

Kamfanin dillancin labaran Reuters da ya ruwaito sanarwar gwamnatin ƙasar Nijar ɗin ya ce kawo yanzu MNJTF ba ta yi tsokaci game da ficewar Nijar ɗin  ba, yana mai ƙarawa da cewa babu tabbas game da yadda matakin zai yi tasiri kan aikin rundunar a nan gaba.

Yankin Tafkin Chadi yana fama da hare-haren ‘yan bindiga ciki har da ‘yan kungiyar ISWAP da Boko Haram, waɗanda suka ƙaddamar da yaƙi a arewa maso gabashin Nijeriya a shekarar 2009 kuma sun kashe dubban mutane.

A bara, Chadi ta yi barazanar ficewa daga MNJTF bayan an kashe sojojinta kusan 40 a wani harin da aka kai wani sansanin soji.

Nijar tana rage hulɗa da wasu maƙwabtanta tun bayan da sojoji suka hamɓarar da gwamantin Shugaba  Mohamed Bazoum a shekarar 2023. Tare da Burkina Faso da Mali – ƙasashe maƙwabta inda sojoji suka karɓe kwanan nan – ta janye daga ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) a shekarar 2024.

Sojojin da ke mulki a Nijar, da suka yi shelar tsarin miƙa mulki na shekara biyar, sun yi alƙawarin tabbatar da tsaro a ƙasar, wadda ‘yan ci-rani da masu safarar mutane ke ƙetarewa ta cikin gagarumar hamadar arewacinta.

Amma sojin ba ta da isassahen iko kan ɓangare da dama na ƙasar, in ji Reuters. Mayaƙa masu kaifin kishin Islama sun kashe aƙalla fararen hula 44 yayin da mutum 13 suka jikkata a wani harin da suk kai kan wani masallaci a kudu maso yammacin ƙasar cikin wannan watan. Kayayyakin samar da makamashinta, ciki har da bututun mai da ya haɗa rijiyoyin man Agadem da gaɓar tekun Benin sun fuskanci hari.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#