Dollar

38,1267

0.1 %

Euro

43,3696

0.65 %

Gram Gold

3.974,4200

0.48 %

Quarter Gold

6.511,6500

0 %

Silver

39,6200

0.06 %

Hukumomi sun ceto fiye da tururuwa 5,000 da aka cunkusa su a cikin mazubai 2,244 a babban filin jiragen sama na birnin Nairobi.

An kama masu fasa-ƙwaurin tururuwa sun cuccusa ƙwarin a cikin kwalaben gwajin jini a Kenya

An kama wasu mutum huɗu da suka yi ƙoƙarin yin fasa-ƙwaurin dubban tururuwa masu rai daga Kenya don sayar da su a kasuwannin dabbobin gida na musamman a Turai da Asiya.

Za a yanke musu hukunci kan safarar namun daji, a wata shari'ar da Hukumar Kula da Namun Daji ta Kenya (KWS) ta bayyana a matsayin wani muhimmin ci gaba.

KWS ta ce hukumomi sun kama tururuwa masu rai, ciki har da nau’in Messor Cephalotes da ake kira Giant African Harvester Ant, waɗanda aka ɓoye su a cikin bututun gwajin gaji da sirinji.

"Bincike ya nuna cewa an tsara bututun gwajin don su iya adana tururuwan har tsawon watanni biyu ba tare da an gano su a filin jirgin sama ba," in ji KWS a cikin wata sanarwa, tana bayyana wannan a matsayin "shirye-shiryen da aka tsara da kyau."

Duk da cewa wasu mutane na ganin tururuwa a matsayin ƙwaro mai ɓarna, akwai masu sha'awar kiwon su a cikin akwatunan gilashi inda za su iya kallon yadda suke gina gidajensu masu rikitarwa.

Takardun kotu da Reuters ta gani sun nuna cewa hukumomi sun kama kimanin manyan tururuwa 5,000 da aka saka a cikin ƙananan robobin ɗaukar jini 2,244, waɗanda darajarsu ta kai kimanin shilling ɗin Kenya miliyan ɗaya ($7,800).

Mutane biyu daga Belgium, ɗaya daga Vietnam, da ɗaya daga Kenya sun amsa laifin mallakar namun daji ba bisa ƙa'ida ba da kuma safarar su, kuma sun bayyana a gaban kotun filin jirgin sama na Jomo Kenyatta a ranar Talata.

"Ba mu zo nan don karya doka ba. Amma saboda kuskure da rashin hankali muka yi," in ji David Lornoy, ɗaya daga cikin masu safarar daga Belgium, yana roƙon kotu ta sassauta musu hukunci.

Kotun ta ɗage shari'ar zuwa ranar 23 ga Afrilu, lokacin da za ta yi la'akari da rahotannin kafin yanke hukunci daga KWS, Gidan Tarihi na Ƙasa na Kenya, da jami'in kula da shari'a. Ana tsare da masu safarar a hannun hukuma.

Wani masanin kasuwancin tururuwa, wanda ya nemi a ɓoye sunansa saboda ƙarancin wannan kasuwa, ya ce masu samarwa suna buƙatar lasisi daga KWS da takardar shaidar lafiya kafin su fitar da Messor Cephalotes.

Masanin ya ce wannan nau'in tururuwa, wadda asalinta daga Kenya ne, ana matuƙar buƙatarta kuma tana da wahalar samu.

KWS ta bayyana wannan shari'ar a matsayin wani muhimmin ci gaba a yaƙin da ake yi da satar halittu, saboda ya haɗa da ƙoƙarin fitar da albarkatun halittu na Kenya ba tare da izini ba ko rabon riba, wanda ya saba wa doka.

"Wannan shari'ar da ba a taɓa ganin irinta ba tana nuna canjin yanayin safarar namun daji - daga manyan dabbobi zuwa ƙananan nau'ikan da ke da muhimmanci ga muhalli," in ji sanarwar.

Wani dillalin musamman daga Birtaniya mai suna AntsRUs ya bayyana wannan nau'in tururuwa a matsayin "abin mamaki sosai idan ana kallonsa."

"Messor Cephalotes suna cikin nau'ikan da mutane da dama ke mafarkin samu. Sarakunan su suna da tsawon kimanin 20-24mm kuma suna da kyakkyawan launin ja da ruwan kasa/baƙi," in ji su.

AntsRUs ta lissafa farashin sarauniya mai rai daga wannan nau'in a matsayin fam 99.99 ($132.44), duk da cewa a halin yanzu ba su da su a ƙasa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#