Sport
Dollar
38,1443
0.45 %Euro
43,5525
0.2 %Gram Gold
4.082,2100
0.46 %Quarter Gold
6.720,2300
0 %Silver
39,9700
0.51 %"A matsayinmu na ƙasar Turkiyya, ba mu da niyyar yin arangama da ko wace ƙasa a Syria, ba ma Isra’ila kawai ba," in ji ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan.
Minsitan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada cewa Turkiyya ba ta da niyyar yin rikici da ko wace ƙasa a Syria, ciki har da Isra’ila.
Yayin da yake zantawa da gidan talabijin ɗin CNN Turk ranar Laraba, Fidan ya yi bayani game da muhimman batutuwa tare da amsa tambayoyi.
"A matsayinmu na Turkiyya, ba mu da niyyar yin arangama da ko wace kasa a Syria, ba ma Isra’ila kaɗai ba," in ji shi, yana mai jaddada cewa Syria ƙasa ce mai cin gashin ganta.
"Ba za a lamunci Isra’ila ta yi ƙoƙarin tsokano Syria ta hanyar amfani da burinta na faɗaɗa a yankin ba," in ji shi.
Fidan ya jaddada cewa Turkiyya ba ta neman rikici da ko wace ƙasa a yankin amma ya yi gargaɗin cewa Ankara ba za ta iya halin ko-in-kula ba idan Syria ta sake fuskantar rashin zaman lafiya a cikin gida, wasu hare-hare ko kuma tsokana da zai iya barazana ga tsaron ƙasa na Turkiyya.
"Ba za mu zauna mu zura ido kawai ba," in ji shi.
Fidan ya kuma soki yadda isra’ila ta ruguza kayayyakin sojin Syria bayan tafiyar gwamnatin Assad da aka hamɓarar, yana mai cewa Tel Aviv ta samar da wata dabarar barin sabuwar gwamnatin Syria da sojojinta da “babu,” kuma tana kai ga wannan dabarar ɗaya bayan ɗaya.
"Ba ma kai hari kan ko wace ƙasar da ba ta yaƙe mu ba. (Amma) idan aka samu wani wuri mai rashin zaman lafiya a wata ƙasa mai maƙwabtaka da zai iya mana illa, ba za mu iya kasancewa ‘yan kallo ba," in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa a irin wannnan yanayi, Turkiyya na ɗaukar matakai, mafi yawa na diflomasiyya.
Da yake amsa wata tambaya game da tafiyar Firayin ministan isra’ila Benjamin Netanyahu zuwa Amurka, Fidan ya ce "A iya cewa Amurka na buƙatar shata layi wa Netanyahu tare da tsara sharaɗi."
Tuntuɓar da Isra’ila
Da yake magana game da tattaunawa kai tsaye ko a kaikaice tsakanin Turkiyya da Isra’ila, Fidan ya ce: "Yayin da muke wasu ayyuka a cikin Syria, za a buƙaci samar da wata hanyar warware rikici a wani lokaci da Isra’ila wadda jiragenta ke shawagi kamar yadda muke da Amurkawa da ‘yan Rasha."
"Akwai abin da za a iya cewa tuntuɓa (da Isra’ila) domin hana masu iya yaƙi su kasa fahimtar juna," in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa ana yin wannna tuntuɓar kai tsaye idan akwai buƙatar yin hakan.
Da yake magana game da dangantakar Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Shugaban Amurka Donald Trump, Fidan ya ce, "Mista Trump yana girmama shugabanmu a matsayinsa na shugaba kuma yana da dangantaka mai kyau da shi."
Da aka tambaya shi game da lokacin da Erdogan da Trump za su iya ganawa, ya ce shugabannin biyu na son yin hakan da zaran dukkansu biyu sun samu sararin ganawa.
Game da ganarwasa da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, Fidan ya ce sun tattauna game da batutuwa da dama, ciki har da buƙatar da ke akwai na dakatar da hare-haren bama-baman da Isra’ila take yi a Syria.
Kasancewa Falasɗinawa a Gaza zai ci gaba da samr da gwagwarmaya
Fidan ya bayyana cewa burin Isra’ila shi ne kada ta bar Falasɗinawa a cikin Gaza da aka yi wa ƙawanya.
"Idan har Falsɗinawa na cikin Gaza, za a ci gaba da samun ‘yan gwagwarmaya — ko irin na salon Hamas ko kuma wani salon na daban. Me zai sa a sami tafiyar gwagwarya? Saboda mamayar na ci gaba. Abin da zai sa ba za a sami wata tafiyar gwagwarmaya ba shi ne a ce an kawar da Falasɗinawa gabaɗaya daga inda suke rayuwa," in ji shi.
"Mun bayyana sharuɗɗa game da daidaita alaƙarmu da Isra’ila. Batun Falasɗinawa na da muhimmanci game da shi.”
Comments
No comments Yet
Comment