Dollar

35,1822

-0.14 %

Euro

36,6623

-0.17 %

Gram Gold

2.963,2100

0.00 %

Quarter Gold

4.908,6300

0.00 %

Silver

33,6200

0.12 %

Continents

Categories

A ƙarshe dai zakaran na Real Madrid Vinícius Júnior ya samu kyauta ta babban ɗan wasa na duniya.

Vinicius Junior ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon FIFA na 2024

Daga ƙarshe dai ɗan wasan Real Madrid Vinícius Júnior ya samu nasarar lashe kyautar babban ɗan wasan duniya a ranar Talata.

An zabi Vinícius a matsayin gwarzon ɗan wasa na na shekara inda ya samu lambar yabo ta FIFA ta "gwarzon bana", yayin da 'yar wasan Barcelona Aitana Bonmati ta ci gaba da riƙe kambun kyautar ta kwallon kafa a ɓangaren mata.

Vinícius ya ji takaicin rashin nasara samun kyautar Ballon d’Or a watan Oktoba, wacce ɗan wasan tsakiya na Manchester City Rodri ya lashe, abin da ya sa Vinícius da ƙungiyarsa Madrid suka yi watsi da bikin da aka yi a birnin Paris, don nuna rashin amincewarsu.

Ɗan wasan na gaba na Brazil ya halarci bikin karɓar lambar yabo ta FIFA bayan da ya tafi Doha ranar Litinin tare da Madrid don buga wasan ƙarshe na cin kofin Intercontinental da Pachuca.

Tauraruwar Bonmati tana haskakawa

Bonmati ta lashe kyautar Ballon d'Or tsawon shekaru biyu a jere, kuma ta lashe gasar La Liga da kofin Sifaniya da kuma gasar Zakarun Turai a Barcelona a shekarar 2024.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet