Dollar

35,1750

-0.15 %

Euro

36,6356

-0.24 %

Gram Gold

2.960,2200

-0.10 %

Quarter Gold

4.908,6300

0.00 %

Silver

33,5600

-0.05 %

Continents

Categories

A damben da aka yi da farko, Usyk ne ya yi nasara bayan ra'ayin alƙalai ya zo ɗaya a makin da suka bayar,  inda Usyk ɗin ya zama gwarzon dambe ajin babban nauyi inda yake riƙe da kambun WBA, WBC da WBO.

Za a sake dambacewa tsakanin Usyk da Fury a Saudiyya

Za a sake dambacewa tsakanin Oleksandr Usyk da Tyson Fury a ranar Asabar da dare a Saudiyya.

A damben da aka yi da farko, Usyk ne ya yi nasara bayan ra'ayin alƙalai ya zo ɗaya a makin da suka bayar, inda ya zama gwarzon dambe ajin babban nauyi. Tun bayan nan ne Usyk ya rabu da kambun IBF wanda a halin yanzu Daniel Dubois yake riƙe da shi.

A halin yanzu wannan damben da za a yi, kambun WBC da WBA da WBO za su zama a kan layi a wurin damben a Riyadh — wanda a nan ne aka yi damben farkon a watan Mayu.

Usyk ya sha da ƙyar a littafin sakamako na alƙalai biyu, 115-112 da kuma114-113. Sai kuma ɗayan alƙalin ya ba su sakamakon 114-113.

Tun daga zagayen farko har zuwa na bakwai, Fury ne a kan gaba a duka sakamakon alƙalan, sai dai daga baya Usyk ya yi ta tasowa. Usyk ya kusan doke abokin hamayyarsa a zagaye na tara, inda ya yi masa kwab ɗaya kafin ƙaraurawar da aka kaɗa ta ceto Fury.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet