Sport
Dollar
35,5594
0.16 %Euro
36,5618
-0.36 %Gram Gold
3.091,7000
-0.06 %Quarter Gold
5.064,8900
0.14 %Silver
34,6700
-1.25 %Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yaƙin da aka shafe watanni 21 ana yi ya haifar da matsalar raba mutane da mahallansu mafi muni a duniya.
Fiye da ‘yan Sudan 55,000 da yaƙi ya raba da gidajensu sun koma yankunansu a sassan jihar Sennar da ke kudu maso gabashin ƙasar, sama da wata guda bayan sojoji sun ƙwace babban birnin jihar daga sojojin sa-kai, a cewar Hukumar Kula da ‘yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
A ranar Asabar, hukumar ta MDD ta ce ma’aikatanta da ke yankin “sun sanya ido kan komawar mutane kimanin mutane 55,466 da suka rasa mahallansu zuwa wurare a faɗin jihar Sennar” tsakanin 18 ga Disamba zuwa 10 Janairu.
A duka faɗin ƙasar kuma, MƊD ta ce yaƙin da aka shafe watanni 21 ana yi ya haifar da matsalar raba mutane da mahallasu mafi muni a duniya, inda fiye da mutane miliyan 12 suka rasa gidajensu.
An ayyana matsalar yunwa a wasu sassan ƙasar, to amma haɗarin na ƙara yaɗuwa zuwa wasu miliyoyin mutanen, ciki har da mazauna yankin arewacin Sennar, kamar yadda wani bincike da ke samun goyon bayan MƊD ya faɗa a watan jiya.
Kwato babban birnin jihar
A watan Nuwamba, Sojojin Sudan da ke yaƙi da sojojin sa-kai na RSF sun ce sun ƙwace iko da Sinja, babban birnin jihar kuma babban wajen da yake haɗa yankunan da sojoji ke iko da su a tsakiyar Sudan da kuma yankin gabashin ƙasar.
Tun watan Yuni RSF ta ƙwace Sinja, lokacin da ta kai hari kan jihar Sennar, inda aka tilasta wa kusan mutane 726,000 tserewa a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya — mafi yawancinsu sun gudo ne daga wasu jihohin.
Yaƙin a Sudan ya kashe dubban mutane.
A ranar Alhamis, Baitul Malin Amurka ya sanya wa shugaban sojoji Abdel Fattah al Burhan takunkumi, yana zargin sojoji da kai hare-hare kan makarantu da kasuwanni da asibitoci, tare da hana samun abinci a matsayin makamin yaƙi.
Takunkumin Amurka
Matakin ya zo ne mako guda bayan Amurka ta sanya wa kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo takunkumi, tana zargin ƙungiyarsa da aikata kisan kiyashi.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce an ɗauki matakin ne kan Dogalo saboda “mummunan keta haƙƙin bil adama” a yammacin yankin Dafur na Sudan “da suka haɗa da yi wa fararen hula da dama fyade da sojojin RSF a ƙarƙashin ikonsa suka yi.”
Comments
No comments Yet
Comment