Sport
Dollar
38,2552
0.34 %Euro
43,8333
0.15 %Gram Gold
4.076,2000
0.31 %Quarter Gold
6.772,5700
0.78 %Silver
39,9100
0.36 %Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da mutuwar mutum 17 a wasu hare-hare biyu da ake zargin makiyaya sun kai kan al'ummomin manoma a jihar ta Benue.
Aƙalla mutum 17 sun rasu bayan wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai hari kan wasu al’ummomi a Jihar Benue, kamar yadda rundunar ‘yan sandan ƙasar ta tabbatar.
Lamarin ya faru ne dai a Gbagir da ke Ƙaramar Hukumar Ukum da kuma a Ƙaramar Hukumar Logo duka da ke yankin Sankera a Jihar Benue.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rikici tsakanin manoma da makiyaya a wasu sassan ƙasar.
A sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sanda reshen Benue Sewuese Anene ta fitar a ranar Juma’a, ta ce ‘yan bindigan sun fara kashe mutum biyar a harin da suka kai Gbagir, inda daga baya kuma wasu ‘yan bindigan kuma suka kashe wasu mutum 12 a Logo.
‘Yan sandan sun yi watsi da rahotannin shafukan sada zumunta da ke cewa an kashe fiye da mutum 100 a harin.
Harin na baya-bayan nan ya faru ne kwana biyu bayan kashe mutum 11 a Otukpo da ke Jihar Benue, haka kuma ƙasa da mako guda bayan an kashe fiye da mutum 50 a Jihar Filato da ke makwabtaka.
Tun daga shekarar 2019, wannan rikicin ya yi sanadin mutuwar rasa rayukan fiye da mutum 500 a yankin da kuma tilasta wa mutum miliyan 2.2 barin gidajensu, kamar yadda wani kamfani da ke bincike na SBM Intelligence ya bayyana.
Comments
No comments Yet
Comment