Sport
Dollar
38,2552
0.34 %Euro
43,8333
0.15 %Gram Gold
4.076,2000
0.31 %Quarter Gold
6.772,5700
0.78 %Silver
39,9100
0.36 %Ofishin mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya yi watsi da jita-jita da ake yaɗawa cewa an hana Shettiman shiga Fadar Shugaban Nijeriya haka kuma an yi masa ɗaurin talala a gidansa har sai Tinubu ya koma Nijeriya.
Ofishin mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa kan cewa an hana shi shiga Fadar Shugaban Nijeriya.
A ranar Juma’a ne wasu labarai suka rinƙa yawo a shafukan sada zumunta inda ake yaɗa cewa wasu jami’an tsaro da aka jibge sun hana Shettiman shiga fadar haka kuma an yi masa ɗaurin talala a gidansa har sai Tinubu ya koma Nijeriya.
Sai dai a martanin da ya mayar game da wannan lamari a ranar Asabar, mai magana da yawun Kashim Shettima, Mista Stanley Nkwocha ya yi watsi labaran inda ya ce ƙarya ce tsagwaranta ake yaɗawa.
Ofishin mataimakin shugaban Nijeriya ya nuna rashin jin daɗinsa game da irin
“A cikin 'yan kwanakin nan, an yi ta yaɗa wasu ƙarerayi dagangan waɗanda aka shirya game da mataimakin shugaban Nijeriya da ofishinsa ta ɓangarori da dama. Irin waɗannan rahotannin da ake haɗawa ana yin su ne da niyyar kawo ruɗani da kuma rikici a Fadar Shugaban Ƙasa. Waɗannan rahotannin na son karkatar da hankulan jama’a domin su amince akwai saɓani a matakin ƙoli na gwamnati,” kamar yadda Stanley Nkwocha ya bayyana sanarwar.
Ya ƙara da cewa mutanen da suke yaɗa waɗannan labaran soki-burutsu ne kawai suke yi domin sun rasa abin faɗa.
Nwokocha ya sake bayar da misali da yadda mutane ke yaɗa ƙarya inda ya ce ko a makon nan sai da fadar shugaban ƙasar ta nesanta kanta daga alluna da fastoci da ake liƙawa na Tinubu da Shettima kan neman shugabancin 2027.
“Waɗannan labaran ƙoƙari ne kawai na taɓa martabar shugaban ƙasa da mataimakinsa da kuma karan-tsaye ga dimokuraɗiyya da kundin tsarin mulki,” in ji shi.
Comments
No comments Yet
Comment