Dollar

38,2552

0.34 %

Euro

43,8333

0.15 %

Gram Gold

4.076,2000

0.31 %

Quarter Gold

6.772,5700

0.78 %

Silver

39,9100

0.36 %

Bayan Allah wadai da ɗabi'un wasu jami'anta da hedkwatar 'yan sandan Nijeriya ta yi, ta ce ta gano fuskokin jami’an da suka karɓi kuɗi daga hannun 'yan China kuma tuni ta ƙaddamar da shirye-shiryen hukunta su.

Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya za ta hukunta jami'an da aka yi wa bidiyo ‘yan China na raba musu kuɗi

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta yi Allah wadai da ɗabi’un wasu jami’anta waɗanda aka gani a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta inda aka ga ‘yan China na raba musu kuɗi.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar, ta bayyana lamarin a matsayin “rashin ƙwarewa da rashin ɗa’a.”

Lamarin wanda ya jawo ce-ce-ku-ce da nuna fushin jama’a a shafukan sada zumunta, ya sa hedkwatar ‘yan sandan ta yi bincike inda ta gano fuskokin jami’an da suka karɓi kuɗin.

Hedkwatar ‘yan sandan ta bayyana cewa tuni ta ƙaddamar da shirye-shiryen hukunci ga jami’an nata.

Hedkwatar ‘yan sandan a sanarwar da ta fitar ta ce ɗabi’un da aka ga ‘yan sandan suna nunawa ba su ba asalin ɗabi’un ‘yan sandan Nijeriya bane.

Ta kuma ce rundunar ba za ta lamunci irin waɗannan ɗabi’un da ke nuna rashin ƙwarewa ba da kuma waɗanda za su jawo musu tofin Allah tsine daga jama’a.

Jami’an ‘yan sandan Nijeriya na yawan jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta inda akasari akan yi musu bidiyo suna karɓar rashawa.

Ko a kwanakin baya sai da rundunar ‘yan sandan ƙasar ta sallami wasu jami’anta biyu masu mukamin kwanstabul kan laifin karbar rashawa daga wata Baturiya.

Haka ma a Disamabr 2024 rundunar ‘yan sandan ta sallami wasu jami’anta 18 kan kama su da laifuka sannan ta rage wa 18 girma.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#