Dollar

38,1137

0.18 %

Euro

42,0543

-0.85 %

Gram Gold

3.708,4600

-2.33 %

Quarter Gold

6.293,2300

-0.18 %

Silver

36,1600

-6.93 %

Wata majiya daga hedikwatar rundunar da kuma wasu majiyoyi biyu daga Fadar Kano da duk suka nemi a sakaya sunayensu sun tabbatar da cewa an aika wa sarkin wasiƙar gayyata, wacce ta samo asali daga sashen Leƙen Asiri na Rundunar ‘Yan Sandan.

‘Yan sanda sun gayyaci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Abuja don amsa tambayoyin kan 'Hawan Sallah'

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gayyaci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II hedikwatarta da ke Abuja don amsa tambayoyi a kan yadda shagulgulan bikin karamar Sallah suka kasance a jihar.

Wata majiya daga hedikwatar rundunar da kuma wasu majiyoyi biyu daga Fadar Kano da duk suka nemi a sakaya sunayensu sun tabbatar wa TRT Afrika cewa an aika wa sarkin wasiƙar gayyata, wacce ta samo asali daga sashen Leƙen Asiri na Rundunar ‘Yan Sandan.

Tun da fari gabanin sallah rundunar ‘yan sanda tare da sauran takwarorinta na tsaro a jihar sun soke duk wani shagali na Hawan Sallah, musamman na hawan dawaki a jihar, saboda dalilan tsaro a cewarsu.

Sai dai a yayin da Sarkin ke tattaki domin halartar Sallah a filin Idi na Kofar Mata a ranar 30 ga watan Maris, an caka wa wani ɗan bijilanti daga cikin masu bai wa sarkin kariya wuƙa inda ya rasu, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Wasu rahotanni sun ce tun da farko Babban Sifeton ‘yan sandan kasar Kayode Egbetokun ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano da ya kama sarkin.

Sai dai kwamishinan ya bayyana wa Sufeto Janar din cewa, lamarin ba shi da alaƙa da keta dokar hana Hawan Sallah, kuma Sarkin bai yi amfani da dawakai wajen ziyartar gidan gwamnati ba a ranar Hawan Nasarawa kamar yadda al’adar ta tanada.

Sai dai watakila Sufeto Janar din bai gamsu da bayanin kwamishina ba, sai ya umurci Sashen Leken Asiri na RUndunar ‘Yan sanda da su kar ragamar binciken tare da gayyatar sarkin zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.

Me wasiƙar ta ƙunsa?

A wata wasikar gayyata da ya CP Olajide Ibitoye sanya wa hannu, rundunar ‘yan sandan ta gayyaci sarkin da ya gurfana a gaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar a Abuja a ranar Talata 8 ga Afrilu da karfe 10 na safe.

“Sufeto Janar na ‘yan sanda ya ba ni umarni, ta hannun Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda na Hukumar Leken Asiri (FID) cewa ana gayyatar ka don bincike kan lamarin da ya faru a lokacin bikin Sallah a yankinka.

“Sakamakon bayanan nan na sama, ana gayyatar ka zuwa sashin binciken sirri na rundunar da ke kallon hedkwatar rundunar ‘yan sanda a unguwar Area 11, Abuja da karfe 10:00 na safe ranar Talata 8 ga Afrilun 2025.

“Kasancewarku a wajen yana da muhimmanci sosai wajen gudanar da bincike mai ma’ana.

“Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda na miƙa maka gaisuwarsa,” in ji wasiƙar.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#