Dollar

38,0195

0.08 %

Euro

41,8561

0.79 %

Gram Gold

3.663,0000

0.6 %

Quarter Gold

6.187,2600

0 %

Silver

36,8500

0.22 %

Wannan sakamakon dai yana nufin Liverpool ce ke saman teburin gasar Firimiya da maki 73 duk da cewa ba ta ƙara ratar da ta bai wa Arsenal da ke biye da ita ba.

Fulham ta doke Liverpool da ci 3-2

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Fulham ta doke Liverpool wadda ke saman teburin a gasar Firimiya da ci 3-2.

Liverpool ce ta fara zura ƙwallo a ragar Fulham ta ƙafar Mac Allister minti 14 da fara wasa kafin Ryan Sessegnon ya rama wa Fulham a minti 23.

Fullham ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sai da ta ƙara wa Liverpool ƙwallo ɗaya a lokacin da ɗan wasan Nijeriya, Alex Iwobi ya zura ƙwallo a ragar Liverpool a minti 32 da fara wasa.

Yayin da ake tunanin cewa Liverpool za ta iya ramawa, sai Fullham ta ƙara mata ƙwallo na uku a lokacin da Rodrigo Muniz ya zura ƙwallo a ragar Liverpool minti 37 da fara wasa.

An dai tafi hutun rabin lokaci Fullham na da rinjaye a kan Liverpool da ci 3-1 yayin da ake tunanin cewa komai na iya faruwa idan aka dawo daga hutun.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Liverpool ta yi ta ƙoƙarin ɗaukar fansa domin ta samu ko da maki ɗaya ne daga wasan, sai dai haƙarta bai cim ma ruwa ba har sai minti 72 da fara wasa.

A minti 72 da fara wasan ne Luiz Diaz ya zura ƙwallo ɗaya a ragar Fullham lamarin da ya mayar da wasan 3-2.

Sai dai kuma Liverpool ba ta iya ƙara wa Fulham ba domin Fulham ta samu ta kare rinjayenta a wasan kuma ta cinye maki ukun wasan gaba ɗaya.

Wannan sakamakon dai yana nufin Liverpool ce ke saman teburin gasar Firimiya da maki 73 duk da cewa ba ta ƙara ratar da ta bai wa Arsenal da ke biye da ita ba.

Ita kuwa Fulham tana ta takwas a teburin gasar Firimiya inda take da maki 48.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#