Sport
Dollar
38,0102
0.08 %Euro
41,5272
0.15 %Gram Gold
3.683,5100
1.16 %Quarter Gold
6.191,9000
0.07 %Silver
37,0600
0.78 %Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abia, Danladi Isa, ya tabbatar wa mutanen jihar cewa za a hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aikar.
Kwamishinan ‘yan sandan Abia da ke kudancin Nijeriya, Danladi Isa, ya tabbatar da kisan da aka yi wa ‘yan ƙasar China biyu da kuma ɗan sanda ɗaya a jihar.
Wannan ya biyo bayan rahoton da rundunar ‘yan sandan jihar ta samu ne cewa wasu ‘yan bindiga sun yi wa wasu ‘yan China kwanton-ɓauna da ‘yan sandan da ke kare su a lokacin da suke kan hanyar zuwa kamfaninsu da ke Agukwu-Amaya, a ƙauyen Ndundu, Uturu, a ƙaramar hukumar Isuikwuato.
Jami’ar hulɗa da jama’a ta ‘yan sandan jihar, Maureen Chinaka, wadda ta bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar ta ce an kashe manajan, Mista Quan da abokin aikinsa Mista Cai da kuma sufeto Audu Saidu (ɗaya daga cikin jami’an ‘yan sanda da ke yi musu rakiya,) a lokacin harin.
Maharan sun yi awon-gaba da bindigar Sufeto Saidu.
Sai dai kuma, rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta yi aikin haɗin gwiwa da soji da sauran hukumomin tsaro, inda ta yi nasarar ceto ‘yan China huɗu da kuma jami’an ‘yan sanda biyu.
Sanarwar ta ce, “bayan mun samu bayanai, jami’ai daga rundunar ‘yan sandan jihar Abia, a wani aiki na haɗin gwiwa da soji da kuma wasu hukumomin tsaro, suka ƙaddamar da aikin neman su.
“Dalilin haka, an ceto ‘yan China uku ba tare da sun ji ciwo ba, yayin da ɗaya ya ji ciwo. Sufeto Uba Ahmed, wanda shi ma an ceto shi, ya ji rauni sakamakon harbin bindiga a ƙafarsa. A halin yanzu ɗan sandan da ya ji ciwo da ‘yan ƙasar wajen suna samun kulawa a asibitin gwamnatin tarayya da ke Abakaliki.
“Yau tawagar jami’an rundunar, a ƙarƙashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (da ke kula da ayyuka), ta ziyarci inda aka aikata laifin a wani ɓangare na aikin nema da ceton waɗanda aka sacen.
“Ta hanyar aikin haɗin gwiwa da ya ƙunshi ‘yan sanda da sojoji da kuma mutanen gari, an ceto sufeto Ijeagwa Friday ba tare da ya ji rauni ba.
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abia, Danladi Isa, ya tabbatar wa mutanen jihar Abia masu kirki cewa za a hukunta waɗanda suka yi aika-aikar.”
Kazalika ya yi kira ga mazauna jihar su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsoro ba kuma su taimaka wa ‘yan sanda ta hanyar ba da bayanai game da mutane ko motoci ko kuma ayyuka da ba su yarda da su ba.
Comments
No comments Yet
Comment