Sport
Dollar
37,9261
-0.12 %Euro
41,1601
-0.07 %Gram Gold
3.788,3800
-0.6 %Quarter Gold
6.210,1600
0 %Silver
41,2900
-0.88 %Alsharaa ya lashi takobin cewa sabuwar gwamnatinsa ba za ta taɓa ƙyale "cin hanci da rashawa su ratsa cikin ma’aikatunmu ba."
An yi bikin bayyana sabuwar gwamnatin Syria inda Shugaba Ahmad Alsharaa ya lashi takobin cewa gwamnatin za ta sake gina ma’aikatu bisa riƙon gaskiya da bayyana gaskiya.
"Muna sanar da samar da sabon mataki a tarihin ƙasarmu, kuma kafa wata sabuwar gwamnati a yau tamkar shela ce ta aniyarmu ta gina sabuwar ƙasa," in ji Alsharaa a wani biki a fadar shugaban ƙasa a Damascus ranar Lahadi.
"Wannan gwanatin za ta nemi buɗe sabbin damarmaki a fannin ilimi da kiwon lafiya kuma ba za mu ƙyale cin hanci da rashawa ya ratsa cikin ma’aikatunmu ba."
Gwamnatin "za ta sake gina ma’aikatun ƙasa bisa riƙon gaskiya da kuma bayyana gaskiya," in ji shi.
Sabuwar gwamnatin ta ƙunshi ministoci 22, ciki har da mace ɗaya.
Ministoci da muƙamansu
Jerin ministocin gwamnatin sun haɗa da ministan tsaro Murhaf Abu Qasra da ministan tsaron cikin gida Anas Khattab da ministan harkokin waje Asaad al-Shaibani da ministan shari’a Mazhar Al-Wais da ministan ilimi mai zurfi Marwan al-Halabi da ministar zamantakewa da ƙwadago Hind Kabawat da kuma ministan kyautan addini Mohammad Abu al-Khair Shukri.
Majalisar ministocin ta kuma haɗa da Hamzah Mustafa a matsayin ministan watsa labarai da Yarob Badr a matsayin shugaban sufuri da kuma Mohammad Eskaf da zai jagoranci ci-gaban gudanarwa. An naɗa Mazen al-Salhani a matsayin ministan yawon buɗe ido, yayin da Mohammad Sameh Hamad zai yi aiki a matsayin ministan matasa da wasanni.
Mohammad Saleh zai ɗauki muƙamin ministan al’adu kuma an naɗa Mustafa Abdul Razzaq a matsayin ministan ayyuka da samar da gidaje.
Ma’akatar ilimi za ta samu jagorancin Mohammad Abdul Rahman Turko yayin da aka naɗa Amjad Badr a matsayin ministan noma.
Abdul Salam Haykal zai kama aiki a matsayin ministan sadarwa da fasahar sadarwa inda aka naɗa Raed al-Saleh a matsayin ministan ba da taimakon gaggawa.
Kazalika cikin majalisar ministocin akwai Mohammad Anjarrani da aka naɗa ministan gudanarwa na cikin gida da Musab Nazzal al-Ali da aka naɗa ministan kiwon lafiya da kuma Nidal Al-Shaar da aka naɗa ministan tattalin arziƙi. An naɗa Mohammad Yusr Barnieh ministan kuɗi yayin da aka naɗa Mohammad al-Bashir a matsayin ministan makamashi.
Ministocin sun gabatar da bayanai kana suka sha rantsuwa a gaban Alsharaa, in ji wakilin kamfanin dillancin labaran Anadolu.
An kafa wata gwamnatin riƙon ƙwarya a ƙarƙshin jagorancin firayiminista Mohammed Al-Bashir na tsawon wata uku bayan dakarun ‘yan adawa ƙarƙashin jagorancin Alsharaa sun kawar da gwamnatin Bashar Assad a watan Disamba. An ayyana Alsharaa a matsayin shugaban ƙasa na riƙon ƙwarya a ƙarshen watan Janairu.
Comments
No comments Yet
Comment