Dollar

37,9278

-0.06 %

Euro

41,2140

0.41 %

Gram Gold

3.806,9700

0.19 %

Quarter Gold

6.332,2600

1.97 %

Silver

41,1600

-1.2 %

Ba a sake bari an shigar da abinci Gaza ba tun farkon watan Maris saboda takunkuman Isra'ila, a cewar UNRWA.

Israila ta kashe yara fiye da 180 a Gaza a rana ɗaya: MDD

Fiye da yara 180 'yan Falasɗinu ne suka rasa rayukansu a hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza a cikin rana guda, a cewar hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijira na Falasɗinu (UNRWA).

“Fiye da yara 180 aka ba da rahoton mutuwarsu a rana guda a Gaza,” in ji hukumar a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.

Sai dai, hukumar ba ta bayyana taƙamaiman lokacin da aka kashe yaran ba.

“Idan ba a dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta ba, za a ci gaba da asarar rayuka da yawa,” hukumar ta yi gargadi.

Rundunar sojin Isra'ila ta ƙaddamar da wani hari ta sama a Gaza ranar 18 ga Maris, inda ta kashe mutum 855, ta raunata kusan 1,900, tare da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni da aka cim ma tun watan Janairu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kiyasta cewa kimanin Falasɗinawa 124,000 ne suka sake rasa matsugunansu tun bayan da Isra'ila ta ci gaba da hare-harenta a Gaza.

“Iyalai a Gaza suna sake tserewa don neman tsira,” in ji UNRWA.

“A lokaci guda, takunkumin da aka ƙaƙaba da ke ci gaba da aiki yana ƙara tsananta matsalar jinƙai. Dole ne a mutunta kuma a kare fararen hula. A kowane lokaci. A ko ina.”

‘Babu abinci, babu ruwa’

Daraktar Sadarwa ta UNRWA, Juliette Touma, ta ce ba a bari an shigar da kayan abinci cikin Gaza ba tun farkon watan Maris sakamakon takunkumin Isra'ila a yankin.

“Tun ranar 2 ga Maris, babu abinci, babu ruwa, babu magunguna, kuma babu kayan kasuwanci da aka bari suka shiga Gaza saboda haramcin Isra'ila,” in ji ta. “Wannan shi ne lokaci mafi tsawo da aka samu hakan tun lokacin da aka fara yaƙin.”

“Kowace rana ba tare da kayan tallafi ba na nufin yara suna kwana da yunwa,” Touma ta yi gargadi.

Fiye da Falasɗinawa 50,200 sun mutu, mafi yawansu mata da yara, sannan sama da 113,900 sun jikkata a munanan hare-haren da sojojin Isra'ila ke kai wa Gaza tun watan Oktoban 2023.

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaronsa Yoav Gallant a watan Nuwamba da ya gabata saboda laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil'adama a Gaza.

Haka kuma, Isra'ila tana fuskantar shari'ar kisan ƙare dangi a Kotun Duniya saboda yaƙin da take yi a Gaza.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#