Sport
Dollar
37,9269
-0.06 %Euro
41,2130
0.41 %Gram Gold
3.808,8700
0.24 %Quarter Gold
6.332,2600
1.97 %Silver
41,1900
-1.14 %Ministan Tsaron Isra'ila Israel Katz ya yi gargadin cewa Hamas za ta fuskanci ta'azzarar hare-hare mai girma, ciki har da sake ƙwace yankuna da kuma lalata abubuwan more rayuwa har sai ta miƙa wuya.
Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya bayyana cewa Isra'ila za ta ci gaba da karɓar ƙarin yankuna a Gaza har sai an kawar da Hamas idan har ƙungiyar ta ci gaba da ƙin sakin sauran Isra’ilawan da take tsare da su.
Ya yi wannan furuci ne a ranar Talata yayin da masu shiga tsakani ke ci gaba da ƙoƙarin ɗabbaka yarjejeniyar tsagaita wuta da aka karya bayan Isra'ila ta sabunta kai hare-haren sama da na ƙasa a ranar 18 ga Maris, bayan gazawar cim ma yarjejeniya kan sharuɗɗan tsagaita wutar.
Isra'ila ta bayyana cewa ba za ta sake amincewa da mulkin Hamas ko ikon soja a Gaza ba, bayan harin da ƙungiyar ta kai a ranar 7 ga Oktoban 2023 wanda ya haifar da yaƙin kisan ƙare dangi daga Isra'ila a wannan ƙaramin yanki.
Sojojin Isra'ila sun bayyana a makon da ya gabata cewa sun fara kai hare-haren ƙasa a tsakiya da kudancin Gaza bayan da suka sake sabunta kai farmaki da hare-haren bama-bamai a yankin da aka killace, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan Falasɗinawa.
Za a ɗanɗana kuɗa
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa manufar waɗannan sabbin hare-hare shi ne tilasta wa Hamas ta saki sauran mutanen da take tsare da su.
"Idan Hamas ta ci gaba da taurin kanta, za ta fuskanci mummunan sakamako wanda zai ƙara tsananta, ta hanyar karɓar ƙarin yankuna (da Isra'ila za ta yi) da kuma kawar da mayaƙa da cibiyoyin ta'addanci har sai ta miƙa wuya gaba ɗaya," in ji Katz a wani bidiyo da kafafen watsa labarai na Isra'ila suka ruwaito.
Sabon harin ya kasance ɗaya daga cikin mafi muni tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-hare watanni 17 da suka gabata, wanda ya karya yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni da aka samu tun ranar 19 ga Janairu.
Hamas har yanzu tana tsare da mutum 59, inda ake tunanin 24 daga cikinsu suna raye, daga cikin fiye da 250 da ta kama a harin da ta kai a ranar 7 ga Oktoba, 2023 a Isra'ila.
Yawancin sauran an sake su ko kuma an mayar da gawarwakinsu ta hanyar musayar yarjejeniya.
Hare-haren soja da Isra'ila ta kai a Gaza ya yi sanadin mutuwar fiye da Falasɗinawa 50,000, a cewar jami'an lafiya na Gaza.
Comments
No comments Yet
Comment