Dollar

38,0350

-0.01 %

Euro

43,2331

0.01 %

Gram Gold

3.940,5400

0.35 %

Quarter Gold

6.469,8500

0 %

Silver

39,5000

-0.2 %

Manyan jami'ai shida sun faɗa wa gidan talabijin na NBC News cewa Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon za ta iya rage rabin sojoji 20,000 ƙari da aka tura Tsakiyar Turai zuwa rabi.

Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Tsakiyar Turai: Rahoto

Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana, matakin da wasu masana ke tsoron zai ƙara wa Rasha karfin gwiwa.

A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tura ƙarin sojoji 20,000 zuwa yankin domin ƙarfafa garkuwar gabashin NATO bayan Rasha ta kai hari Ukraine.

A ranar Talata, NBC ta ruwaito cewa jami’ai shida daga Amurka da Turai sun tabbatar da tattaunawa kan rage yawan sojojin da aka tura, inda aka fi mayar da hankali kan rage adadin a Romania da Poland.

Shugaba Donald Trump yana ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe fiye da shekaru uku a Ukraine cikin gaggawa tun bayan hawansa mulki, amma har yanzu bai cim ma nasarar warware matsalar ba.

Ya sha sukar NATO, yana mai jaddada cewa ya kamata Turai ta ɗauki ƙarin nauyi wajen kare kanta ta hanyar ƙara kashe kuɗi kan harkokin tsaro, da kuma jagorantar samar da makamai ga Ukraine.

Duk wani rage yawan sojojin Amurka zai ƙara wa Shugaba Vladimir Putin na Rasha ƙwarin gwiwar shiga cikin al’amuran Turai ta hanyoyi daban-daban, in ji Seth Jones daga Cibiyar Nazarin Dabarun ƙasa da ƙasa ga NBC.

A halin yanzu, akwai kimanin sojojin Amurka 100,000 da ke Turai, inda 65,000 daga cikinsu ke zama a nahiyar ta dindindin, yayin da sauran suke aiki a matsayin ma’aikatan da ale da kuma karin karfi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#